Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Na Tattaunawa Akan Daukan Sabbin Matakan Ladabtar Da Kasar Eritrea


Tattaunawar kwamitin sulhun MDD akan daukan sabbin matakan ladabtar da kasar Eritrea.
Tattaunawar kwamitin sulhun MDD akan daukan sabbin matakan ladabtar da kasar Eritrea.

Eritrea ta dora laifin yin kaimin daukan matakan a kan abokiyar gabar ta Ethiopia.

Kwamitin Sulhun MDD na shirin duba yiwuwar daukan sabbin matakan ladabtar da kasar Eritrea bisa zargin ta da neman tada zaune tsaye a kasashen da ke makwaftaka da ita.

A yau talata kwamitin Sulhun mai wakilai 15, ya kamata ya fara tattauna shawarwarin haramta zuba jari a masana’antar hakar ma’adinan kasar Eritrea, sannan ya kara daukan wasu matakan haramta yin balaguro ga shugabannin kasar kuma a kama kadarorin su da ke kasashen waje.

A shekarar dubu biyu da 9 kwamitin sulhun ya kafa dokar haramta cinikin makamai da Eritrea, da kuma daukan matakan takurawa wasu shugbannin kasar saboda zargin da aka yiwa kasar cewa tan a tallafawa ‘yan gwagwarmayar Islamar kasar Somaliya.

Kwanan nan sashen MDD mai lura da karfafa matakan ladabtarwar a kan kasar Eritrea, ya fada cewa Eritrea ce ta shirya wata makarkashiyar neman farfasa boma-bomai a wurin taron kolin kungiyar kasashen Afirka a Ethiopia a cikin watan janairun da ya gabata.

Eritrea ta musanta zargin cewa ta na goyon bayan ‘yan tawayen kasar Somaliya, kuma ta musanta cewa ta na da hannu a cikin makarkashiyar neman kai harin bom din, sannan kuma ta yi kira ga kwamitin sulhun MDD cewa ya cire dukkanin matakan ladabtarwar da ya dauka a kan kasar.

Eritrea ta dora laifin yin kaimin daukan matakan a kan abokiyar gabar ta Ethiopia, wadda su ka yi shekaru biyu su na fafata yakin kan iyaka , daga shekarar 1998 zuwa shekarar dubu biyu.

XS
SM
MD
LG