Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD ta Nemi Gwamnati da 'Yan Tawaye a Sudan ta Kudu su Tsagaita Wuta


Babban sakataren majalisar dinkin Duniya Ban Ki-moon.
Babban sakataren majalisar dinkin Duniya Ban Ki-moon.

Babban magatakardar MDD Ban ki-moon, yana kira ga ‘yan tawayen da gwamnatin Sudan ta kudu su amince kan shirin tsagaita wuta ba tareda wani bata lokaci ba.

Babban magatakardar MDD Ban ki-moon yana kira ga ‘yan tawayen da gwamnatin Sudan ta Kudu su amince kan shirin tsagaita wuta ba tareda wani bata lokaci ba.

Da yake magana a wani taron manema labarai jiya jumma’a, Mr. Ban yace ya bukaci shugaba Salva Kiir ya karfafa shawarwarin wanzarda zaman lafiya ta wajen amincewa da daya daga cikin manyan bukatun ‘yan tawaye. Sakataren na MDD yace yayi magana da Mr. Kiir inda ya bukace shi ya nuna dottaku da sassauci ta wajen sakin fursinonin siyasa.

Sai dai gwamnatin Mr. Kiir taki ta saki fursinonin siyasa 11 da take tsare da su kamar yadda ‘yan tawayen suka bukata. Ana jin wanan batun shine ya janyo cikas a shawarwarin sulhunda ake yi a a Ethiopia.

Kwamitin sulhu na MDD shima a jiya jumma’a yayi kira ga Mr. Kiir da ya saki fursinonin siyasar, kuma ya roki duka sassan biyu su tsaida fada nan take.

Ana ci gaba da kwabza fada tsakanin ‘yan tawaye da sojojin gwanati cikin kasar, inda jiya jumma’a sojojin kasar suka kwace garin Bentiu babban birnin jihar Unity wacce da take hanun ‘yan tawaye.

Kakakin sojojin sudan ta kudu Phillip Aguer ya gayawa wani shirin talabijin na sashen turanci anan Muriyar Amurka cewa sojojin kasar yanzu suna dannawa kan Bor, fadar jihar Jonglei dake hanun ‘yan tawaye.

Daya daga cikin madugun ‘yan tawaye Birgediya janar Lul Ruai Koang, yace ‘yan tawaye sun janyene daga Bentiu domin kada fadan ya rutsa da farar hula. Yace har yanzu ‘yan tawaye suna ci gaba da rike Bor da kuma rijiyoyin mai dake jihohin biyu.
XS
SM
MD
LG