Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Ministar Zirga-zirgar Jiragen Sama Zata Yi Da Motoci Masu Sulke?


Masu aikin ceto bayan faduwar jirgin sama a Najeriya
Masu aikin ceto bayan faduwar jirgin sama a Najeriya

Yayin da Najeriya ke fama da faduwar jirage sama sai gashi ministar ma'aikatar ta kashen dimbin miliyoyin nera sayen motoci masu sulke.

Kwana kwanan nan 'yan Najeriya suka fusata da ministar ma'aikatar zirga-zirgan jiragen sama da ma'aikatar domin faduwar wani jirgin da irin kalamun da suke fito daga bakinta. Amma kuma sai gashi zargin kashe makudan kudi wurin sayen motoci biyu masu sulke wai domin kare lafiyarta ya kunno kai .

Amincewa da ma'aikatar zirga-zirgar jiragen sama ta yi na kashe dalar Amurka miliyan daya da digo shida ($1.6) ko kwatankwacin nera miliyan dari biyu da hamsi (N250m) bai hana kungiyoyin dake yaki da cin hanci da rashawa kiran Stella Oduah ministar ma'aikatar ta yi murabus ba. Bayan da shugabannin yaki da cin hanci da rashawa irinsu Rotimi Fashakin suka ce ta sauka domin irin wannan zarmiya ke sanadiyar faduwar jiragen sama wani shugaban wata kungiya kuma tsohon dan majalisa Bina Mailayi ya ba ministar sa'o'i arba'in da takwas ta yi murabus. Ya ce ta ajiye aiki domin rashin imani aka yiwa 'yan Najeriya kuma sun yi Allah Ya isa. Kudin da ta kashe ya ce a mayar dasu nan da zuwa ranar Talata. Idan ba'a mayar da su ba zasu fantsama yin zanga-zanga. Ya ce sun san cewa ministar tana kusa da shugaban kasa kuma sun sa ido su ga abun da zai yi.

Wai an sayo motocin ne domin kare lafiyar ministar daga wadanda suke yi mata barazana domin kin jinin sauye-sauyen da ta ke yiwa ma'aikatar. Tun da labarin sayen wadannan motocin masu dan karen tsada ya fito mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu to amma abun ya kara tsamari bisa ga irin kalamun da ministar ke yi na cewa shege ka fasa.

Ga Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye


LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG