Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Ya Hana Kasashen Larabawa Sa Baki A Rikicin Israila Da Falasdinawa?


Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce wasu abubuwa uku ne su ka sa kasashen Larabawa yin gum da bakin su game da ruwan wutan da Israila ke yiwa Falasdinawa

Kwana shida kenan Israila na ruwan wuta a Zirin Gaza. A yayin da Majalisar Dinkin Duniya da ma Amurka ke kokarin shiga tsakani a tsagaita wuta, kasashen Larabawa da kasashen Musulmi sun ja bakin su, sun yi gum ba me cewa komi.

A kan haka ne Babban Editan Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha na Sokoto ya tuntubi kwararren masani harakokin yankin Gabas ta Tsakiya, kuma Malamin Addinin Islama, Sheikh Aminu Daurawa na Darul Sunnah Islam Foundation a Najeriya:

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kan rikicin Israila da Gaza.-3':01"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye


Idan ba a manta ba dai Israila ta kaddamar da kai hare-haren kan Zirin Gaza ne bayan kisan wasu matasa uku Yahudawa da ake zargin kungiyar Hamas da aikatawa.

Israila ta ce ta na kai hare-haren ne domin ta kare kan ta daga rokokin da Falasdinawa ke harba ma ta.

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya na kira ga bangarorin biyu da suka kai zukata nesa kuma su tsagaita wuta.

XS
SM
MD
LG