Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin jama'a a kasar Phillipines sun saurari hudubar Paparoma Francis

Paparoma Francis a filin saukar jiragen saman Tacloban, kasar Pillipines
Paparoma Francis a filin saukar jiragen saman Tacloban, kasar Pillipines

Miliyoyin jama'a ne suka taru yau Lahadi a Manila baban birnin kasar Phillipines domin ganin Paparoma Francis a yayinda zai yi huduba a waje. Paparoman zai yi huduban ne a yayinda yake kamalla ziyarar kwanaki biyar daya kai yankin.

Jami'an kasar Phillipines sun kiyasta cewa kimamin mutane miliyan shidda ne zasu kasance a gandun Rizal na Manila, karkashin luran jami'an tsaro dubu hamsin.
Tilas Paparoman ya arcewa mahaukaciyar guguwar teku a birnin Tacloban, watani goma sha hudu bayan da mahaukaciyar guguwar teku Haiyan au ta kashe ko kuma ta sa fiye da mutane dubu bakwai da dari uku bacewa.
Kadawar iska tayi karfi sosai, a lokacinda Paparoman ke jawabi harma wata ma'aikaciyar coci ta mutu a lokacinda wani abu ya fadi akanta.
Paparoman wanda ya isa kasar Phillipnes a ranar Alhamis yace ya kai ziyarar ce domin ya nuna yadda yake jinjinawa wadanda bala'in mahaukaciyar guguwa Haiyan ta yiwa barna ko kuma ta rutsa dasu a watan Nuwamban shekara ta dubu biyu da goma sha uku.
Paparoman ya kuma tabo wasu batutuwa a lokacin ziyara tasa, domin ya fadawa shugaba Benigno Aquino da sauran shugabani a birnin Manilla a ranar Juma'a cewa su yi watsi da anobar cin hanci da rashawa

XS
SM
MD
LG