Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mukalar Yusha'u Kan Minista Ngozi Iweala


Ministar kudi ta Najeriya Ngozi Okonjo Iweala
Ministar kudi ta Najeriya Ngozi Okonjo Iweala

Mukalar da ta sa aka yiwa wani jami'in yada labarai Yusha'u ritayar dole.

Ngozi Okonjo-Iweala da Sarkakiya a Nada Mukamai-Yusha'u A. Shuaib
Har yanzu ina mamakin yadda ministar sha'anin tattalin arziki da har ila yau kuma itace ministar kudi, Dr.Ngozi Okonjo Iweala ke cikin rikici. Amsa sunan mukamai biyu da ta ke yi ba iya yi ba ne kamar yadda wassu za su yi tunani. Kasancewar ta ta farko da ta hau kan irin wannan mukamin a tarihin Najeriya; za a dauki mukamin na ta tamkar na Firayin minista ce wanda hakan ya ba ta hurumin sanya ido kan harkokin dukkan ma'aikatu,sassan gwamnati da hukumomi.Hakan ya hada da duba ware mu su kasafin kudin su, da yadda su kan samarda kudin shiga. Ba shakka itace mai mukami ma fi tasiri a majalisar zartaswa in ka debe shugaba Jonathan da mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo.

A shekaru goma da su ka shude, marubucin wannan makala na daga cikin wadanda ministar ke burge su don nasarorin ta kan samun zurfin ilimi da kwarewar aiki a matakin duniya da gudunmawar da ta bayar wajen bunkasar tattalin arzikin Najeriya, kasancewar ta mace ta farko da ta taba zama ministar kudi daga bisani kuma ministar harkokin waje karkashin gwamnatin Olushegun Obasanjo a 2003 da 2006.Duk da dai ta bar gwamnati ba shiri saboda wassu dalilan kashin kai amma sannan dai ta bar mukamin da ake ganin ta tabuka abun kirki.

Babban abun da wasun mu ke ganin cancantar aikin Dr.Ngozi Iweala shine yadda ta yi tafiya tare da idon gari a 'yan kudu da arewa lokacin da ta ke kan ministar kudi daga 2003-2006.Ba a taba kushe ta da nuna wariya don banbancin kabila a gagarumar kasar da ke da kabilu da addinai daban-daban.Hakanan ma a ka yiwa uban gidan ta shaida a wancan lokacin da duk da 'yan matsaloli da ya ke da su,amma dai bai nuna kabilanci ba. Shugaba ne da ba ya kabilanci,kuma ya na da kishin kasa da amanna da wanzuwar Najeriya.

Wadanda ta ke ba da sunayen su don samun mukamai sun fito ne daga dukkan sassan kasar har ma da wadanda su ke cikin kwamitin tan a tattalin arziki kamar Nasir Elrufai.Nuhu Ribadu,Bode Augusto,Dr.Mansur Muktar,Chukwuma Soludo da sauran su.

Nasarorin ta ma na da ban sha'awa.Za mu iya tunawa a 2005 ta jagoranci Najeriya wajen tattaunawa da cibiyar bas hi ta Paris Club wacce ta biyawa Najeriya wani sashen bashin da a ke bin ta da ya kai dala biliyan 12 inda wajen biya a ka sharewa kasar dala biliyan 18. Ta tabbatar da adalci a rabiyar kudi ga jihohi ta hanyar wallafa yadda a ke rabiyar duk wata a wassu zababbun jaridu.

Da wadannan nasarorin bai zama wani abun mamaki ba da ta samu gagarumin goyon baya daga dukkan 'yan Najeriya lokacin da shugaba Jonathan ya sa ke nada ta a matsayin ministar kudi da kuma sanya sunan ta a 2012 cikin ma su neman mukamin shugabar bankin duniya.Wani dandalin labaran ta yanar gizo ma ya ruwaito cewa wassu mallaman musulmi na addu'a a masallatai don samun nasarar Ngozin.A wancan lokacin duk an dauka ba ta da kabilanci ga kuma kwarewar aiki.
Dalilin wannan rubutun shine ankaradda ita ga wassu nade naden mukamai da ke da sarkakiya ta hanyar yin illa a siyasance da kuma ta fuskar tattalin arziki.Na yi tsammanin za ta ci gaba da halin kwarai a matsayin ta na ministar da ta fi tasiri ga shi kuma gimbiyar Igbo ce daga yankin Neja Delta don kasancewar ta 'yar Obi na Ogwashi-Uku-a jihar Delta.

Kwanannan kungiyar hadin kan yarbawa (Yoruba Unity Forum) ta yi zargin ana tsame hannayen yarbawa daga mukaman gwamnatin tarayya karkashin mulkin shugaba Jonathan.Bayan taron kungiyar a Ikenne jihar Ogun, Bishop ta majami'ar katolika ta Akure (mai ritaya) Rt.Reverend Bolanle Gbonigi ta yi zargin gwamnati da gangan ta ke tsame hannayen yarbawa daga mukaman gwamnatin tarayya bata hanyar adalci ba. Sun yi kira ga gwamnatin da ta daina wannan matakin da gangan don yarbawa sun fara kulewa da lamarin gwamnatin.

Ba a dade ba daga lokacin da yarbawa su ka yi wanann kukan sai kungiyar 'yan majalisar dattawa na arewa ta koka ga yadda ba a adalci wajen dauka da Karin girma ga sojoji.Dattawan sun nuna damuwa da yadda su ka ce a ke nuna rashin adalci da bawa 'yan kabilar Igbo fifiko a wannan bangaren wanda ya saba da tsarin rabon mukamai na kasa.

Ya kamata ta san cewa 'yan Najeriya na tuna bayanan da ta yi a littafin mawallafi Chinua Achebe mai taken "Teacher of Light" inda ta nuna bacin rai ga yadda a ka nunawa kabilar ta wariya yayin da bayan yakin basasa.Don haka a ke rade-radin tun da yanzu ta shigo gwamnati ta ke kokarin gyara wannan tunanin da ta ke yin a nuna wariya ga al'ummar ta.Wassu ma sun dage cewa abun da ta ke yi yanzu shine karfafa ajandar bangaranci da kabilanci da ked a illa ga sauran yankunan Najeriya ta hanyar murdiya wajen nadin mukamai.

A gaskiya ma dai an ambaci sunan ta a baya-bayan nan da hada kai da wata mai babban mukami a gwamnati don sake nada Mrs.Aruma Oteh a matsayin shugaban hukumar kasuwar hannayen jari duk da zargin badakalar da a ke yi ma ta da ma kira da majalisa ke yi na a tsige ta daga mukamin ta.Okonjo Nweala dai ta tsaya kai da fata kan matsayin ta da ya sa har yau Oteh ke kan mukamin ta daram.

Yayin da muhawara kan Oteh bai gama sanyi ba,wata gamayyar matasa karkashin jagorancin dan rajin kare hakkokin bani adama Shehu Sani, ta kalubalanci dalilan nada sabon shugaban hukumar tara kudaden shiga ta kasa alhali wani dan arewa Kabir Mashi na kan mukamin kuma ya na bunkasa hanyoyin samun kudin shigar hukumar. A karkashin Mashi hukumar ta tara haraji musamman a shekarar kudi ta 2012 da ya kai NAIRA ZAMBAR MILIYAN DUBU BIYAR INDA CIKI NAIRA ZAMBAR MILIYAN DUBU DAYA DA MILIYAN DARI TAKWAS (KASHI 36.07 CIKIN DARI) su ka fito daga kudaden harajin da ba su shafi man fetur ba.

Kungiyar ta nuna kwamitin day a bincika lamarin hukumar tara kudin shigar da a ka nuna don tabbatar da adalci ne bagaye kawai don ya na cike ne da dimbin dangin ta ne 'yan kabilar Igbo.Su ka kara da cewa "Ba mu yi amannar cewa an nuna adalci ba,mu na togaciya ga shugaban kasa da ya gujewa sarayar da hakkin shugabancin sa ga ministar kudi.

A zahiri sun zarge ta da nuna kabilanci a yawancin mukaman da ta nada tun dawowar ta kan wannan mukamin.Wassu daga mukaman da su ka yi zargin ta nada 'yan uwanta sun hada da shugaban hukumar kula da kadarorin gwamnati,hukumar kula da kampanonin sadarwa NCC kazalika har ma da nada wata mata mai shekaru 40 a matsayin shugabar hukumar pansho ta kasa.

Mutane na mamakin yadda yak an zamanto 'yan kabilar Igbo ne ke nasara a duk jarrabawar daukar aiki mai muhimmanci da ta gudanar ta hanyar wassu kungiyoyin duniya da ta zaba da kan ta don gudanar da jarrabawar. Abun da kawai ke nuna adalci a daukar ayyukan shine daukar wassu shugabannin sassa na wucin gadi da aikin sun a jeka na yi ka ne ta irin rind a za su bayar.

Amfani da kalmomin gwada daukar aikin kamar "SAI MAFIYA KWAKWALWA" "SAI WADANDA SU KA SAMU HORARWA A KETARE" 'SAI KWARARRU MAZAUNA KETARE" hanya ce da kan hana kwararrun 'yan Najeriya neman irin mukaman da hakan kan gurgunta ci gaban kasa.Nuna cewa wassu mukaman sai kwararru daga wata kabila ne za su iya ya zama wajibi a gyara wannan tsari.

Da yawa a kan samu wadanda su ka samu kwarewar a ketare bas a tabuka abun kirki fiye da wadanda su ka kware a cikin gida musamman a lamurra ma su tsauri.
Ya zama wajibi Dr.Ngoji ta fahimci cewa daukar kwararru daga kebabbiyar kabila zai jawowa wadanda a ka daukar mummunar kiyayya daga sauran sassa kamar yadda ya faru a 1960s inda yawancin wadanda a ka dauka aiki a matakin tarayya su ka fito daga wata kabila.

Ga irin mu da mu ka amince da cewa har yanzu ministar na da cancantar aiki,ya zama wajibi ta nesanta kan ta daga zargin aiki don cimma burin 'yan Biafara (ma su son raba Najeriya) a wajen nadin mukamai.Mu na zamanin mulkin dimokradiyya ne da bai dace a rika gudanarda lamurra ta hanyar kama karya na tunanin "Yanzu al Zamanin Mulkin Mu Ne."

Don haka na ke bukatar ta ta rika tabbatar da cewa a na nada mukaman ne bisa cancanta da zai gamsar da mizanin al'umma. Na yi amannar cewa sai ma su son kasa da alheri ne kawai za su iya fitowa su fadi gaskiya yadda mutane ke dubayadda lamurra ke gudana a kasar nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:11 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG