Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmai Da Krista Sun Yi Bude Baki A Pilato


Mutane suna zanga zanga a Jos
Mutane suna zanga zanga a Jos

Kungiyar tsofofin dalibai na jihar Pilato da suka yi karatu a kasar Amurka ta shirya taron bude baki tsakanin Musulmai da Krista.

Kungiyar 'yan asalin Pilato da suka yi karatu a kasar Amurka ta shirya hidimar bude baki tsakanin Musulmai da Krista a Pilato domin jawo hankalinsu su fahimci juna su kuma koma da cigaba da irin zaman lafiyar dake tsakaninsu can baya.

Jagoran kungiyar Mr. Ezekiel Gomos ya bayyana dalilin shiya taron. Ya ce sun shirya taron domin inganta zumunci, su fada ma juna gaskiya, su kuma gafartawa juna domin a koma yadda ake da can. Ya ce idan ba'a zauna tare ba to ba za'a san abubuwan dake damun kowane bangare ba. Zasu cigaba da yin irin wannan taron a lokuta daban daban da ma bita.

Musulman da suka halarci taron shan ruwan sun yaba da kokarin kuma sun yi farin ciki. Sun bada tabbacin hadin kai domin samun zaman lafiya da aka yi yanzu ya dore. Shugaban kungiyar Krista reshen Jos Ta Arewa shi ma ya ce ya yi murna kuma ya dauki alkawarin tara duk fastoci ya fadakar da su domin cigaban zaman lafiya. Da yake mayarda martani Kwamishanan Labarai na Jihar Pilato Abraham Yiljap cewa ya yi harakar tsaro ko zaman lafiya ba na mutum daya ba ne. Abun da kungiyar ta yi abun koyi ne ga kowa. Shi ma kwamandan rudunar soji ya ce akwai wadanda basa son zaman lafiya domin suna kudi da rikicin. Don haka ya kira mutane da su guje ma masu son tada zaune tsaye.

Zainab Babaji nada rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG