Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Hudu Sun Mutu A Wani Harin Da Aka Kai A Jihar Filato


Wasu sojojin Nijeriya kenan ke kokarin tabbatar da tsaro a wasu rikice rikicen da su ka auku a baya.
Wasu sojojin Nijeriya kenan ke kokarin tabbatar da tsaro a wasu rikice rikicen da su ka auku a baya.

An sami asarar rayuka da na dinbin dukiyoyi sanadiyyar aukuwar wani tashin hankali a garin Kuka da ke Karamar Hukumar Shendam ta jihar Filato.

An sami asarar rayuka da na dinbin dukiyoyi sanadiyyar aukuwar wani tashin hankali a garin Kuka da ke Karamar Hukumar Shendam t
a jihar Filato da misalin karfe biyar na yammacin jiya Asabar.

Galadiman garin na Kuka Hashim Ali ya gaya ma wakiliyarmu ta Jos Zainab Babaji cewa jiya Asabar da misalin karfe hudu da minti da ashirin da shida sai kwatsam su ka ji harbe harben bindiga don haka sais u ka gudu zuwa wurin sojoji, wadanda duka-duka ba su wuce sha daya a garin ba. Amma da wutar ta yi yawa sai sojojin su ka ce suma abin ya fi karfinsu. Anan nan sai ga gudunmowar sojoji daga garin Sarkin Kudu a jihar

Taraba, wadanda su ka taimaki sojojin da ke garin su ka fatattaki maharani. Y ace da su ka shiga duba abubuwan da su ka biyo bayan harbe harben sai su ka ga gawarwakin mutane hudu.

Shi ma wani mai suna Attahiru Muhammad ya ce sun yi jana’izar mutane hudu banda wadanda su ka bace kuma wayoyinsu basu kadawa. Y ace kuma an kona gidaje sama da dari uku. Y ace a yanzu haka sun yi gudun hijira zuwa Yalwan Shendam da Kuanpan da jihar Taraba.

Shi kuma Kantoman Karamar Hukumar Shendam Ezekiel Affan ya ce bayan da hukuma ta sami labarin tashin hankalin sai maza ta tura jami’an tsaro don su taimaki sojoji da ‘yan sandan da ke garin. Ya ce ana kuma cigaba da daukar duk matakan da su ka dace don shawo kan komai. Amma ya ce ba a sami maharan ba.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG