Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla 81 Aka Tabbatar Sun Mutu a Masallacin Jumma'a na Kano


U.S. President Barack Obama holds a baby during his visits at Iwakuni Marine Corps Air Station, enroute to his Hiroshima trip in Iwakuni, Japan.
U.S. President Barack Obama holds a baby during his visits at Iwakuni Marine Corps Air Station, enroute to his Hiroshima trip in Iwakuni, Japan.

Bama-bamai sun tashi yayin da ake sallar Jumma'a a Babban Masallacin Kano, birni mafi girma a yankin arewacin Najeriya

Mutane akalla 81 ne aka tabbatar sun mutu a bayan fashe-fashen bam da kuma harbe-harben da suka biyo baya a cikin harabar Masallacin Jumma'a na Kano. Wannan al'amari a Masallacin dake shake da jama'a, ya faru a daidai lokacin da aka tayar da Sallar Jumma'a.

Shaidu suka ce sun ga gawarwaki da yawa da kuma wadanda suka ji rauni a bayan da wasu bama-bamai biyu suka tashi a harabar Masallacin, yayin da na uku ya tashi a nan kusa.

Tarzoma ta barke a bayan tashin bama-baman. 'Yan sanda sun tinkari matasan da suka dauko duwatsu da sanduna. Kamfanin dillancin labaran Reuters yace sai da 'yan sanda suka harba barkonon tsohuwa kafin suka samu shiga cikin Masallacin.

Wani wakilin VOA yace hankula sun kwanta bayan nan a yayin da ma'aikatan kiwon lafiya suka fara kula da wadanda suka ji rauni.

Wannan masallaci dai yana kofar fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sunusi na Biyu, daya daga cikin manyan shugabannin Musulmi, wanda a kwanakin baya yuayi kira ga jama'a da su rika tsayawa su na yakar 'yan Boko Haram.

Babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin a birni na biyu wajen girma a Najeriya, amma an fara zaton aikin kungiyar Boko Haram ce wadda ta kai irin wadannan hare-hare a baya.

A halin da ake ciki, hukumomi a Jihar Borno sun gano wani bam da aka dana kusa da wata kasuwa a Maiduguri, suka warware ta kafin ta tashi. A ranar talata an kashe mutane da dama a harin kunar bakin wake a wannan kasuwar.

XS
SM
MD
LG