Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Fiye da 32,000 Ne Suka Kamu da Cutar Kwalara a Kasar Habasha


Mutanen da fari ya shafa suna jiran taimakon ruwa da abinci
Mutanen da fari ya shafa suna jiran taimakon ruwa da abinci

Ethiopia na fama da barkewar gudawa wacce ta kama fiye da mutane 32,000. A lokaci guda kuma, tsohon ministan lafiya na kasar Tedros Adhanom Ghereyesus shine dan wakilin kasar a cikin mutanen dake takarar shugabancin Hukumar Kiyon Lafiya ta duniya wato W-H-O a takaice.

Lamurra biyu yanzu sun hadu waje guda da yake wasu masu nazari na zarginsa da kin bayyana gaskiyar cewa wannan cutar da ta barke a yanzu Kolera ce, wanda yin hakan zai iya yin lahani ga tattalin arzikin Ethiopia.

A yau Litinin ne kasashe 194 dake da wakilci a cikin hukumar lafiya ta duniya zasu hadu a Geneva domin tattaunawa na tsahon kwanaki 10 wanda za’a fara yau Litinin.

Abu na farko da zasu fara kuwa aiwatarwa shine zaben shugaban hukumar WHO na gaba.

Tedros yana daya daga cikin mutane dake takarar shugabancin hukumar wadanda har ila yau suka hada da mutane biyu daga kasashen Birtaniya da Pakistan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG