Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane sun soma tsokaci akan tafiye tafiyen Shugaba Buhari


Shugaban Jamus tare da Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Jamus tare da Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Tsohon dan majalisar dattawa Babayo Gamawa na jam'iyyar PDP ya jajantawa gwamnatin Buhari kuma bai ga laifin yawan tafiye tafiyen da shugaban ke yi zuwa kasashen waje ba.

A makon jiya ne shugaba Buhari ya dawo daga hutun kwana biyar amma yanzu ya nufi kasar Masar saboda halartar taron tattalin arzikin nahiyar Afirka.

Shi ma shugaban ya kare yawan tafiye tafiyensa da cewa hakan nada riba ga Najeriya wajen farfado da tattalin arziki tare da dawo da barayin biro suka jibge a ketare.

Wannan muhawara ta suka ko goyon bayan shugaban tana fitowa ne yawanci daga 'yan siyasa. Umar Lamido Tetare dake ganin PDP ta kama hanyar nasara da zaben Modu Sherif a matsayin shugabanta na ganin tafiye tafiyen Buharin sun wuce gona da iri. Yace duk shekaru biyar da Jonathan ya yi yana mulki baki daya bai wuce kwanaki 57 ba da ya yi a waje. Amma cikin watanni takwas da Buhari yayi a mulki ya yi fiye da kwanaki 150. Ya kare da cewa a shekarar 2019 jam'iyyar PDP zata kadashi.

Amma dan rajin kare muradun APC Shuaibu Malambura yace tafiyar Buharin tana da matukar anfani. Zuwansa zai zo da kwararru da zasu sa Najeriya hanyar cigaba.

Saidai masana kan tattalin arziki basa korafi kan tafi tafiyen shugaban amma sun damu da rasa kafa kwamitin tattalin arziki.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG