Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Iraqi Sun Yi Watsi da Barazana


Al’ummar kasar Iraqi a yau laraba, sun yi watsi da barazanar tashe-tashen hankulan dake addabarsu suka je rumfunan zabe domin kada kuri’arsu a babban zaben da aka gudanar irinsa na farko tun janyewar sojin Amerka a shekarar 2011.

An zagaye dukkan inda rumfunan zaben suke domin hana tashin hargitsi da baiwa masu kada kuri’ar damar zaben duk wanda vsuke son zaba daga cikin ‘yan takarar dubu tara da suke takarar kujeru 328 na Majalisar dokokin Iraqi.

Sai dai duk tsauraran matakan tsaron da aka dauka da tulin jami’an ‘yan sandan dake kewaye da inda ake jefa kuri’a saida aka sami tashin hankali a birnin Bagadaza.

Duka-duka dai ance mutane goma sha daya ne suka rasa rayukansu a duk fadin kasar ta Iraqi a dalilin tashe-tashen hanulan dake da nasaba da siyasa.


Gefe daya kuma jami’an tsaron Iraqin sun bada rahoton tashin boma-bomai a gefen titunan mota amma duk basu hana ‘yan Iraqi zuwa rumfunan zabe domin kada kuri’unsu ba.

Friminista Nouri al-Maliki na takarar kujerar friminista a zagaye na uku,ya sami sukunin kada tasa kuri’ar a yau laraba a rumfar dake birnin Bagadaza, sannan yayi kira ga ‘yan Iraqi da suma suje rumfunan zabe domin sauke nauyin dake kansu.
XS
SM
MD
LG