Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Misra sun yi zanga-zangar nuna bacin ransu game da gazawar matakan tsaro bayan tashin halin da ya biyo bayan wasan kwallon kafa


Masu zanga-zangar nuna rashin amincewa da gazawar bangaren tsaro a tashin hankalin wasan kwallon kafar Port Said
Masu zanga-zangar nuna rashin amincewa da gazawar bangaren tsaro a tashin hankalin wasan kwallon kafar Port Said

Dubban ‘yan Misra sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu

Dubban ‘yan Misra sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da gazawar jami’an tsaro wajen hana tashin hankali a wajen gasar kwallon kafa da ya kai ga mutuwar akalla mutane 74 da kuma raunatar daruruwar mutane a birnin Port Sa’id da ke arewacin kasar.

Wasu masu zanga-zangar sun taru a yau dinnan Alhamis a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin al-Kharira a sa’ilinda wasu kuma su ka yi maci zuwa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da ke kusa da wurin, a inda ‘yan sandan kwantar da tarzoma su ka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa su.

Wani taron jama’a kuma ya yi ta ihun gwale gwamnatin ta mulkin soja a tashar jirgin kasar birnin al-Khahira ta inda wadanda su ka tsira daga yamutsin na ranar Laraba ke isowa gida, wasunsu da raunuka.

Firayim Minstan Misra da soji su ka nada wato Kamal al-Ganzuri y ace gwamnati ta rushe Hukumar Kwallon Kafar Misra ta kuma dakatar da gwamnan Port Sa’id da kuma shugabannin bangarorin tsaro a matsayin martanin faruwar wannan bala’in, wanda ya na daya daga cikin mafiya muni a tarihin wasannin motsa jiki.

Aika Sharhinka

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG