Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Tafawa Balewa Sun Mika Takardar Kuka


Tawagar ta tsame hannunta daga yunkurin da wakilin yankin a majalisar wakilan tarayya yake yi na ganin an sake maida hedkwatar karamar hukumar zuwa garin Tafawa Balewa

Wata tawagar al'umma daga yankin karamar hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi, ta yi tattaki zuwa harabar majalisar dokokin jihar, domin mika takardar kukar da suka nemi a damkawa shugaban majalisar wakilan tarayyar Najeriya, Aminu Tambuwal, game da abinda suka bayyana a zaman take-taken da ba su yarda da su ba na wakilin yankin a majalisar tarayya.

Kakakin wannan tawaga, Malam Ibrahim Mohammed, yace su na son su bayyana adawarsu da yunkurin da Malam Yakubu Dogara, dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Tafawa Balewa da Bogoro da Dass, yake yi a majalisar na neman ganin an sake maido da hedkwatar karamar hukumarsu zuwa garin Tafawa Balewa.

Kwanakin baya ne majalisar dokokin Jihar Bauchi, ta yi dokar da ta dage hedkwatar karamar hukumar daga garin Tafawa Balewa zuwa garin Bununu, a wani mataki na kawo karshen fadan da ya ki ci ya ki cinyewa da aka yi ta gwabzawa na kabilanci da addini a garin Tafawa Balewa.

Ga rahoton Abdulwahab Mohammed daga Bauchi kan yadda wannan batu ya kaya a harabar majalisar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG