Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Wukari na Kukar Dokar Hana Fita Waje Sosai


Mukaddashin gwamna Garba Umar ya ziyarci garin na Wukari yayin da jama'a ke kukar karancin abinci da ruwan sha a dalilin hana kowa fita

Al'ummar garin Wukari sun koka da matsanancin halin da suka shiga na rashin wadatar abinci da ruwan sha a saboda dokar da aka kafa ta hana fita waje baki daya a garin a bayan wani mummunan tashin hankalin da yayi sanadin kashe mutane da dama tare da hasarar dukiya mai yawa.

Wani jami'in kungiyar agaji ta Red Cross dake taimakawa mutanen garin na Wukari, Mr. Lucky Abio, yace mutane su na cikin matukar bukatar abinci da ruwa da kuma magunguna a saboda ba su da sukunin fita waje domin sayen wadannan abubuwa.

Yace a saboda babu kowa a waje, wasu bata-gari su na fasa kantunan mutane su na musu sata, don haka yana da kyau a kyale mutane su samu zarafin fita ko da na gajeren lokaci ne domin su samo abinci da kayan bukatu.

Shi kansa mukaddashin gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Garba Umar, ya bayyana cewa bai ji dadin abinda ya gani ba a lokacin da shi da manyan jami'an gwamnatinsa da na tsaro suka ziyarci garin na Wukari.

Mukaddashin gwamnan ya jajanta wa mutanen na Wukari bisa abinda ya faru, yana mai cewa gwamnati zata kara kaimin samarwa da matasa aikin yi domin rage irin wannan rikicin.

Aku Uka na Wukari, kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Taraba, Dr. Shekarau Angyu, ya bayyana takaicin wannan rikici na Wukari, sannan ya roki gwamnati da ta sassauto da dokar hana fita da aka kafa.

Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta ce mutane 21 ne aka kashe a wannan rikici, yayin da aka kama 24.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG