Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutumin farko da ya fara sa kafa a duniyar wata ya rasu


Wani dan sama jannati Buzz Aldrin tsaye gaban tutar Amurka
Wani dan sama jannati Buzz Aldrin tsaye gaban tutar Amurka
Mun sami labarin mutuwar mutum na farko da ya soma saka kafarsa akan Wata, watau neil Armstrong.

Iyalin mamacin sunce a yau Assabar ne wannan dan sama-jannatin, 82, ya rasu a garin Cincinnati bayan wata rashin lafiyar da ta soma kama shi a farkon watan nan.

Neil Armstrong shine wanda yayi jagiorancin Kumbun Apollo 11 da ya sauka a kan Wata a ran 20 ga watan Yulin 1969. A wannan lokacin ne yayi wani kalamin da ya shiga tarihi inda, lokacinda ya dora kafarsa akan watan ya kada baki yace “wannan wani dan kankanen mataki a wurin mutum guda, amma gagarumin mataki ne a wurin halittar Bil Adaman duniya.”

Duniya ta tsaya cik tana kallon Armstrong yana wannan tattakin tareda dan’uwansa dan sama-jannati, Edwin “Buzz” Aldrin.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG