Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutuwar Sarkin Da Yafi Kowanne Sarki Dadewa Yana Sarauta


Sarkin Thailand
Sarkin Thailand

Shugabannin kasashen duniya na ta ci gaba da aika sakkonin ta’azziya bayan mutuwar sarkin da akace yafi kowane sarki dadewa yana sarauta a duniya, watau Sarki Bhumibol Adulyadej, sarkin kasar Thailand.

wanda ya rasu yana da shekaru 88 a duniya, wanda akuma akace galibin mutanen kasarshi su milyan 67 basu taba sanin wani sarki ba, bayansa a duk rayuwarsu.

Marigayin sarki Bhumibol dai ya hau gadon sarautar kasar tasu yana matashi dan shekaru 18 ne kacal a shekarar 1946 – ma’ana ya share zunzurutun shekaru 70 ke nan cur yana sarautar kasar ta Thailand!

XS
SM
MD
LG