Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Hukumar Kwastam Ta Kama Kayan Abinci Da Aka Yi Fasa Kwaurinsu


Hamid Ali Mai Ritaya Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya
Hamid Ali Mai Ritaya Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya

Hukumar Kwastam a Najeriya mai kula da jihohin Oyo da Osun, ta kama Shinkafa da Man girki da kuma Tayoyin mota na miliyoyin Naira da aka yi fasa kwaurinsu.

Mataimakin kwantirola, Bayero Tanko Mohammed, ya ce hukumar ta kama motar tirela dauke da shinkafa buhu 600, sai kuma wasu kanana motaci uku dake dauke da buhunan shinkafa 150. Da kuma wata mota dauke da Man girki da ta tayoyin mota.

Baki daya motocin an kama sune cikin dare a sassa daban-daban na jihohin Oyo da Osun, biyo bayan samun wasu bayanan sirri da hukumar ta yi, a cewar Bayero Tanko.

Kamar yadda hukumar kwastam ta saba a duk lokacin da sukayi babban kamu, zata gurfanar da mutanen da aka kama gaban kotu domin a tuhumesu da taka dokar ‘kasa na shigar da kaya ba tare da bin hanyoyin da suka kamata ba.

Yin fasa kwaurin kayan abinci da sauran kayayyakin amfani na yau da kullum ya zama ruwan dare a Najeriya, sai dai hukumoni na gargadin al’umma dangane da yin amfani da su, domin rashin sanin ingancin musamman ma kayan abinci.

Domin karin bayani ga Hassan Umaru Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG