Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Shirin Fara Janyo Mai daga Nijar


Bututun Man Fetur
Bututun Man Fetur

Kamfanin matatar mai na Najeriya, NNPC na duba yuwuwar fara janyo dayen man fetur da sauran albarkatunsa daga Jamhuriyar Nijar.

Wannan mataki na zuwa ne, lura da yadda ake samun katsewar samar da danyan mai daga yankin Niger Delta mai arzikin mai zuwa matatar mai ta Kaduna, sanadiyar hare-haren tsagerun yankin.

Rahotanni sun yi nuni da cewa yayin wata ziyara da ya kaiwa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i, shugaban matatar man ta NNPC, Mai Kanti Baru, ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dukufa wajen ganin an nemi mafita dangane da samar da man.

Bayanai sun yi nuni da cewa tuni hukumomin Najeriya suka fara tuntubar takwarorinsu na Nijar domin ganin yadda za aiwatar da wannan aiki.

Aikin dai ya hada har da dasa butatan mai, ta yadda za a rika turo man daga Nijar zuwa matatar man ta Kaduna arewacin Najeriya.

Ibrahim Ka’almasi Garba ya yi hira da Engineer Khailani Muhammed, tsohon ma’aikacin matatar mai ta NNPC, kan alfanu da akasin hakan game da wannan yunkuri:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:21 0:00

XS
SM
MD
LG