Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Shugaba Buhari Zai Tafi Hutu


Shugaba Mohammadu Buhari
Shugaba Mohammadu Buhari

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai tafi hutu har na tsawon kwanaki goma daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairu.

A wata wasika da shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya karanta a zauren majalisa, ya sanar da cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shine zai gudanar da lamuran ‘kasa a lokacin da Buhari ya tafi hutu.

Wata takarda da fadar shugaban ‘kasa ta aikewa manema labarai, na nuna cewa a lokacin wannan hutu da shugaba Buhari zai dauka, zai je ganin likita domin a duba lafiyarsa kamar yadda aka saba duk shekara.

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa shugaban kasa damar sanar da shugaban Majalisar Dattawa da na Wakilai kafin ya dauki hutu.

XS
SM
MD
LG