Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Dauki Matakin Saukaka Samun Visar Shiga Kasar


Ministan tsaron cikin gidan Najeriya Janar Abdulrahaman Danbazau da hukumar shige da fice ke karkashinsa
Ministan tsaron cikin gidan Najeriya Janar Abdulrahaman Danbazau da hukumar shige da fice ke karkashinsa

Matakin saukaka samun visa da gwamnatin Najeriya ta bullo dashi yana da nasaba ne da shirin bunkasa saka jari domin fita daga karayar tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

A sanarwar da ta fito daga ofishin ministan yada labarun Najeriya Lai Muhammad masu saka jari zasu huta da dogon turancin samun visar

Za'a saukaka lamarin da bukatar bada visar gaggawa daga filayen jiragen sama. Masu saka jari ko yawon shakatawa da bude ido na iya shigowa Najeriya koda kasarsu bata da ofishin jakadancin Najeriya.

Kafin wannan sabon shirin masu aiki a Najeriya ko zuwa taro ko yin wani abu sukan fuskanci wuya kafin su sami visa. Sabbi kuma basu da tabbas.

Hukumar shige da fice ta kara bude ofisoshi 28 a fadin kasar domin saukin samun littafin tafiya, wato, fasfo sanadyar sauya suna ko ga mata da suka yi aure ko kuma bacewar littafin.

Shugaban hukumar shige da fice Muhammadu Baban Dede yace sun horas da ma'aikatansu akan yin anfani da naura mai kwakwalwa ta zamani. Yace sun tsara fasfo din ta yadda babu wani da zai iya wallafa na jabu.

Masana tattakin arziki kan yawan nanata mahimmancin zuwan masu saka jari a kasar a daidai wannan lokacin.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG