Accessibility links

Hukumomin kula da shige da ficen baki sun ce yanayin tsaro da kuma kusantowar zabe a shekara mai zuwa suka sanya su daukar wannan matakin

Najeriya ta kori wasu bakin haure kimanin 700 a wani bangare na kokarin murkushe wadanda ake zaton ‘ya’yan wata kungiyar tsagerancin addini ce.

Babban jami’in hukumar kula da shige da ficen baki a Jihar Borno, Babayo Alkali, ya fada jiya alhamis cewa bakin da aka kora ba su da cikakkun takardun zama a kasar, kuma sun fito ne daga kasashen Nijar da Kamaru da Chadi. Yace korar mutanen ta zamo dole a saboda halin tsaron da ake ciki a Jihar Borno da kuma zaben shugaban kasa dake tafe a shekara mai zuwa.

Alkali bai ambaci kungiyar nan ta Boko Haram ba, wadda aka dora ma laifin kai wasu hare-hare a cikin ‘yan watannin nan a arewacin Najeriya. Hare-haren sun hada da wadanda aka kai kan caji ofis na ‘yan sanda da kuma harbe ‘yan sandan. Akasarin wannan fitina ta wakana ne a Jihar Borno. An girka sojoji a yankin a dalilin hakan.

XS
SM
MD
LG