Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: 'Yan Majalisun Wakilai Na Neman A Baiwa Yahya Jammeh Mafaka


Shugaba Mohammadu Buhari
Shugaba Mohammadu Buhari

Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta bada shawarar cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari yaba shugaban kasar Gambia dake fama da matsin lamba, Yahya Jammeh mafaka.

‘Yan majalisar Wakilan Najeriya sun tatttauna kan kudurin da aka gabatar jiya Alhamis a cikin matakan da ake dauka na neman hanyoyin mika mulki cikin ruwan sanyi a karamar kasar dake Afrika ta yamma.

'Dan majalisar Wakilai Mohammed Zorro, shi ne ya gabartar da tayin mafakar a zauren majalisa, da yace, Alheri ne ga Najeriya ta taimaka wajen ganin an mika mulki lafiya a Gambia.

Yace, matakan diplomasiya da aka saba 'dauka ke nan a ko’ina a ba wadanda suke gudun hijira mafaka. Dalili ke nan muke so mu bada gudummuwarmu a majalisa, domin karawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari karfin gwiwa.

Ana rade radin cewa, mai yuwuwa ne Jammeh yana kokarin ci gaba da mulki ne domin gujewa tuhuma. Ana zarginsa da taka hakin bil’adama cikin shekaru 22 da ya shafe yana mulki. Za a iya bashi mafaka a Najeiya da nufin shawo kan Jammeh ya sauka daga karagar mulki, inji wani fitaccen 'dan fafatuka a Abuja, Echezona Asuzu.

Asuzu yace, "zasu iya sauke shi daga karagar mulki daga nan su fara neman hanyoyin da zai amsa laifukan da ya aikata. Wannan yana cikin matakan siyasa."

Asuzu mai rajin damokaradiya ne. yana ganin tayin afuwar mataki ne mai kyau, sai dai yana shakkun kulla irin wannan yarjejeniyar da Najeriya.

An ba tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor mafaka a Najeriya a wani yanayi mai sarkakiya sama da shekaru goma sa suka shige, daga baya aka mika shi domin a tuhumeshi a Saliyo.

Najeriya ta ba shugabannin Afrika da dama mafaka da suka hada da Felix Malloum, tsohon shugaban kasar Chadi, da tsohon shugaban kasar Samaliya Mohammadu Siad Barre.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG