Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Zata Kashe Daruruwan Dubban Miliyoyin Naira Don Ceto Kamfanonin JIragen Sama


Gwamnatin Najeriya ta ce zata kashe Naira miliyan dubu dari biyar domin ta ceto kamfanonin safarar jiragen saman kasar dake cikin kasadar wargajewa.

Gwamnatin Najeriya za ta kashe kimanin dala miliyan dubu uku da dari uku, ko kuma Naira miliyan dubu dari biyar, domin ceto kamfanonin safarar jiragen sama na cikin kasar dake fuskantar matsaloli.

Wani kakakin Babban Bankin Najeriya, Mohammed Abdullahi, ya ce wannan kudin zai ba wadannan kamfanonin safarar jiragen sama sukunin sake sabunta basussukan dake kawunansu, su koma na tsawon shekaru 10 zuwa 15.

Babban Bankin na Najeriya yace ya dauki wannan matakin ne domin sassauto da irin nauyin bashin dake kan wadannan kamfanoni. Kamfanonin safarar jiragen sama sun bunkasa a Najeriya cikin 'yan shekarun nan, amma da yawa daga cikinsu su na shan wahala a saboda gasa mai zafi da suke fuskanta da kuma tsadar man jirgin sama.

Abdullahi yace wannan tallafin da za a yi zai kuma taimaka ma su kansu bankunan Najeriya saboda zai hana kamfanonin safarar jiragen saman kasa biyan basussukan da bankunan suke binsu.

A bara, Najeriya ta bayar da tallafin fiye da dala miliyan dubu biyu da dari biyar, ko kuma Naira miliyan dubu dari uku da saba'in da biyar, domin ceto wasu bankunan kasar su 5.

XS
SM
MD
LG