Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Nemin Tallafin China Wajen Bunkasa Samar Da Kayan Bukatu


Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a lokacin da yake shiga fadar White House a Washington, Alhamis, 31 Maris, 2016
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a lokacin da yake shiga fadar White House a Washington, Alhamis, 31 Maris, 2016

Ziyarar shugaba Muhammadu Buhari a China zata nemi tallafi a fannonin wutar lantarki, hanyoyin mota, jiragen kasa da na sama da kuma samar da ruwan sha da gidaje a fadin Najeriya.

Fadar Aso Villa ta shugaban Najeriya ta sanar da cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi kokarin neman karin tallafin kasar China wajen bunkasa samar da kayayyakin bukatu na yau da kullum a Najeriya, musamman a fannonin wutar lantarki, hanyoyin mota, jiragen kasa, zirga zirgar jiragen sama, samar da ruwan sha da kuma gidaje, a ziyarar da zai kai kasar daga gobe lahadi.

Wata sanarwar da mai ba shugaban shawara kan hulda da kafofin labarai, Femi Adesina, ya bayar, ta ce shugaba Buhari zai tattauna da shugaba Xi Jinping, da Firimiya Li Keqiang, da shugaban majalisar dokokin kasar, Zhang Dejiang.

Ana sa ran za a rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama na bunkasa cinikayya da huldar tattalin arziki a tsakanin Najeriya da China a lokacin wannan ziyarar. Yarjejeniyoyin sun hada da wadda ma’aikatar masana’antu da cinikayya da zuba jari ta Najeriya zata rattaba ma hannu da Hukumar Raya Kasa da Sauye Sauye ta China kan bunkasa masana’antu da samar da kayan bukatu a Najeriya.

Shugaba Buhari da tawagarsa zasu kai ziyara zuwa yankin walwalar cinikayya na Shanghai da Yankin Bunkasa Tattalin Arziki na Guangzhou domin ganewa idanunsu yadda kasar ta China ta yi amfani da wadannan manufofi da shirye-shirye wajen samun bunkasar tattalin arzikinta cikin gaggawa, da nufin aiwatar da irin wannan a Najeriya.

Sanarwar fadar Aso Villa ta ce wadanda zasu rufa ma shugaba Buhari baya a wannan ziyara sun hada da gwamnonin wasu jihohi, da kuma ministoci masu yawa, cikinsu har da na noma, da na albarkatun ruwa, da na sufuri, da na tsaro, da na wutar lantarki, da na ayyuka da gidaje, da na masana’antu, da na kimiyya da fasaha, da na babban birnin tarayya Abuja, da kuma na harkokin waje.

Shugaba Buhari zai bude wani taron bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari tsakanin Najeriya da China a birnin Beijing, sannan zai gana da ‘yan Najeriya dake zaune a can.

A karshen mako mai zuwa zai koma gida.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG