Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Takali Muhimman Matsalolin Tattalin Arziki


Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya yana jawabi a Port Harcourt
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya yana jawabi a Port Harcourt

Ministan harkokin kudi na Najeriya yace sabuwar gwamnatin kasar zata takali muhimman matsalolin tattalin arziki, ciki har da batun samar da ayyukan yi da kyautata samar da rance mai sauki.

Ministan harkokin kudi na Najeriya, Olusegun Aganga, ya ce sabuwar gwamnatin kasar ta kuduri aniyar tinkarar muhimman matsalolin tattalin arziki, ciki har da rashin ayyukan yi da samar da rance mai sauki.

Mr. Aganga ya ce ceto bankunan kasuwanci datsabar kudi dala miliyan dubu 4 da Babban Bankin Najeriya yayi a shekarar da ta shige, abu ne na bajimta. An kafa sabuwar Hukumar Kula da Kadarori domin ta saye basussukan da wadannan bankuna suka bayar aka kasa biyansu domin su bankunan su samu sabbin kudaden gudanarwa har su biya wani bangaren da Babban bankin ya bayar don ceto su.

Sai dai kuma matakin ceto bankunan ya kara tsaurin matakan bayar da rance, har ma shugabannin kasuwanci da jama'ar kasar sun ce su na shan wahala wajen samun rance a yanzu. Idan har ma suka samu, sun ce wani lokacin kudin ruwan da suke biya yana kaiwa har kashi 20 cikin 100.

Watanni biyu a bayan kama aikinsa, Aganga yace yana da matukar muhimmanci ga kananan kamfanoni da masana'antu su samu rance mai sauki. Tsohon jami;in na bankin zuba jari na Amurka da ake kira Goldman Sachs yace hakan zai taimakawa Najeriya ta rage rashin ayyukan yi, inda a yanzu kusan kashi 20 cikin 100 na al'ummar kasar ba su da aiki.

Ministan kudin ya ce, "Babban abin damuwa a nan ma shi ne matasa masu hsekaru 15 zuwa 24 ko 25 su ne suka fi fama da rashin aiki, inda a manyan birane kimanin kashi 50 cikin 100 na wadannan matasa ba su da aiki, sai kuma kashi 40 cikin 100 a karkara."

Babban Bankin Najeriya ya bude wani asusu na kudi fiye dala miliyan dubu 3 domin taimakawa bankuna wajen sabunta basussuka ga masana'antu, da kamfanonin safarar jiragen sama da kuma masu samar da wutar lantarki. Rashin wutar lantarki a kai a kai, na daya daga cikin abubuwan dake tauye tattalin arzikin Najeriya, kasar da ta fi kowacce man fetur a Afirka. Sabon shugaban kasar, Goodluck Jonathan, ya dora ma kansa alhakin kyautata wutar lantarki a kasar.

Habaka wutar lantarki na daya daga cikin alkawuran marigayi shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa, kuma ya hs asuka saboda kasa cimma wannan alkwarin har zuwa rasuwarsa a watan da ya shige.

A saboda haka, kasada ce ga shugaba Jonathan ya alakanta kansa sosai da batun bunkasa wutar lantarki ganin cewa ya rage masa saura kasa da shekara guda a kan mulki. Amma idan har zai samu nasarar samar da wutar lantarki, to masu fashin bakin siyasa sun ce tana iya samar masa da farin jinin da zai iya lashe zaben shugaba a shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG