Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na'urar NASA Ta Hango Duniyar Farko Mai Kama Da Tamu


Wannan hoton, zane ne na yadda masana kimiyya suke tsammanin duniyar Kepler-22b zata iya kasancewa.
Wannan hoton, zane ne na yadda masana kimiyya suke tsammanin duniyar Kepler-22b zata iya kasancewa.

Wannan duniya da aka lakabawa suna Keppler-22B ita ce ta farko da aka taba gani a yankin da za a iya samun ruwa mai gudana a doron duniyar

Kungiyar masu bincike ta Kepler ta Hukumar Bincioken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA, ta bayarda sanarwar gano Duniya ta farko wadda ke cikin wani yanki na kewayen ranarta inda ruwa mai gudana zai iya kasancewa a kan doronta.

Na'urorin da kungiyar Kepler ta yi amfani ad su sun hango curin duwatsu masu kewaya ranar da take kusa da su da yawa, wadanda a Hausance muke fassarawa da duniya, amma kuma ba su taba hango wata duniyar da ta yi kama da wadda muke cikinta ba.

Ita wannan duniyar da aka tabbatar da kasancewarta bayan da aka kara yin bincike, wadda aka sanya mata suna Keple-22b, ita ce karama daga cikin wadanda aka hango su na shawagi a tsakiyar inda ruwa zai iya kasancewa a kewayen wata rana mai kama da ta duniyar Bil Adama.

`Misalin inda duniyar Kepler-22b take kewaya ranarta cikin yankin da ruwa zai iya kasancewa a sama, da misalin yadda duniyar Bil Adama take a kasa
`Misalin inda duniyar Kepler-22b take kewaya ranarta cikin yankin da ruwa zai iya kasancewa a sama, da misalin yadda duniyar Bil Adama take a kasa

Duniyar ta Kepler-22b, ta ninka girman duniyar bil Adama sau biyu da kusan rabi, sai dai har yanzu masana kimiyya ba su san ko doronta duwatsu da kasa ne, ko ruwa ne ko kuma dai gas ne ba. Sai dai su na bayyana kwarin guiwar cewa wannan matakin farko ne a ci gaba da kokarin gano ko akwai duniyoyi masu kama da ta Bil Adama a cikin sararin subhana.

Masana kimiyya na Kungiyar Kepler a hukumar NASA su na amfani da na'urorin hango cikin samaniya dake nan doron kasa da kuma wata na'urar hango cikin samaniya mai suna Spitzer wadda aka harba ta can cikin samaniya domin su sake nazari da aunawa da kuma duba alamun duniyoyi masu kewaya taurari a can sama wadanda na'urar hangen nesa ta Kepler ta hango.

Ita na'urar ta Kepler, tana zura ido a kan tauraro daya a lokaci guda, domin ta ga ko akwai wani curin da zai kewaya shi. Ita wannan na'ura sai ta ga curin ya kewaya wannan tauraro har sau uku, kafin ta tabbatar da cewa lallai duniya ce mai kama da tamu dake kewaya ranarta. Idan ta gano hakan, sai a yi amfani da na'urori a nan doron kasa da kuma a samaniya a zura ido kan wannan tauraro a sake dubawa domin tabbatar da abinda na'urar hangen nesa ta Kepler ta gani.

Kepler-22b tana da matukar nisa daga nan duniyar bil Adama. Haske ma, ko walkiya, zai dauki shekaru 600 daga nan duniya kafin ya kai can. Koda yake Kepler-22b ta fi duniyarmu ta bil Adama girma, kwanaki 290 take yi kafin ta kewaya ranarta, watau shekara guda a doronta kw3anaki 290 ne. Ranarta ma tana kama da ranarmu a nan duniyar bil Adama.

Daga cikin curin duwatsu masu kama da duniya guda 54 da aka gano su na zagaya taurarinsu a inda za a iya samun ruwa mai gudana, duniyar Kepler-22b ita ce ta farko da aka tabbatar da kasancewarta. Za a bayyana wannan ci gaban da aka samu a cikin mujallar nan ta kimiyyar samaniya mai suna Astrophysical Journal.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG