Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIGER: An dage bukin FIMA Bisa Dalilan Tsaro


Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar yana jawabi.
Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar yana jawabi.

A jamhuriyar nijer masu tsare tsaren bukin baje kolin madimkan nafiyar afrika (FIMA) da ya kamata a soma a gobe laraba a birnin yamai sun bada sanarwar dage wannan buki zuwa wata ranar da ba a bayyana ba saboda dalilan tsaro.

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun bayyana cewa, sun yanke shawarar dage bukin FIMA karo na goma ne, bisa dalilan tsaro, biyo bayan harin ta’addancin da aka akai a makon jiya a birnin bamako na kasar mali da wadanda aka kai mako guda kafinsa a birnin paris na kasar faransa wadanda suka haddasa asarar rayukan mutane da dama .

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar tace ta dage wannan buki domin taya makwafta juyayin abinda ya samesu sannan tace matakin zai taimaka a kara karfafa kwanciyar hankali saboda haka tace wajibi ne jama’a su bada hadin kai.

Bakin da suka dako gari daga kasashen duniya daban daban domin halartar wannan buki na FIMA sun bayyana matukar kaduwa da jin sanarwar dage wannan haduwa ta kasa da kasa.

A gobe laraba 25 Nuwamba ya kamata a soma wannan buki sai dai a maimakon jawabin kaddamarwa gwamnatin Nijer ta hanyar kakakinta za ta sanarda jama’a matakin dage bukin a hukumance.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Sule Mumuni Bama ya aiko daga Nyamie.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG