Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Iya Yin Asarar Dala Biliyan 8 Kan Cutar Shanyewar Sashin Jiki Da Sauransu


Wani mutum mai fama da cutar sashin jiki
Wani mutum mai fama da cutar sashin jiki

Gwamnatin tarayya ta kiyasta cewa a cikin shekaru 10 masu zuwa, zata yi asarar kudaden da suka kai dala bilyan 8 sakamakon mutuwa ta dalilin shanyewar sashen jiki da kuma wadansu cututtuka idan ba’a dauki matakan da suka wajaba ba.

Gwamnatin tarayya ta kiyasta cewa a cikin shekaru 10 masu zuwa, zata yi asarar kudaden da suka kai dala bilyan 8 sakamakon mutuwa ta dalilin shanyewar sashen jiki da kuma wadansu cututtuka idan ba’a dauki matakan da suka wajaba ba.

Ministan lafiya, Farfesa Onyebuchi Chukwu, ya fadi wannan a ranar bukin shanyewar sashin jiki na duniya, mai taken, “domin na damu akai.”

A wannan taron da kungiyar cutar shanyewar sashin jiki ta Nigeriya ta shirya, ministan ya ambaci kiyascin da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayas domin ya jaddada abin da yake fada.

Ya kara da cewa, ya zuwa yanzu hasarar dukiyar da kasar take yi sakamakon ciwon zuciya, shanyewar sashin jiki da ciwon suga kadai, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta kiyasta a a shekara ta 2005, sun kai na dala miliyan 400.

Ministan yace shanyewar sashin jiki ita ce ke kawo kwantar da mafiya yawan masu cutar jijiyoyin jiki a asibiti a Nigeriya wanda kuma ya kan zama sanadiyar mutuwar kasha 40 zuwa 50 cikin dari cikin watanni uku na gano wannan matsalar.

Yace, “wani bincike da aka yi a wata ma’aikata ya nuna cewa kashi 39 cikin dari na wadanda suka rayu bayan wata uku suna mutuwa a cikin wata 12, kana kuma sauran kashi 12 cikin na wadanda suka rage sukan sami wata mummunar nakasa.”

Bisa ga fadar ministan, shugaba Goodluck Jonathan, ya dauki wannan damuwa ta cutar shanyewar sashin jiki da mahimminci, ya kuma nuna wannan ta kaddamar da shirin yi a ranar 9 ga watan Nuwamba wanda ya nemi ya zuga yan Nigeria da su rika binciken lafiyarsu akai akai su kuma kula da yadda suke gudanar da rayuwarsu.

Chukwu yace an yi amfani da wannan take, “domin na damu akai” a shekarar da ta wuce, ya kuma nuna cewa dawo da wannan taken wannan shekarar yana nuna muhimmancin da wannan yake da shi wajen kare shanyewar sashen jiki, kulawa da kuma goyawa wadanda suka sami kansu cikin wannan matsalar baya

Ya na mai cewa, “Wannan kungiya ta shanyewar sashin jiki ta bamu dama domin mu dubi taken kamfen na ranar duniya ta wannan cutar: “domin na damu akai”. Haka kuma kungiyar ta jawo mu kusa domin ta nuna mana cewa za’a iya daukar matakan kare shanyewar jiki kuma za’a iya lura da masu ita. Zanso in nanata cewa domin ka damu akai, dole ka kaunaci zuciyarka domin ka kiyaye kwakwalwarka.”

Tun farkon a cikin kalamanta, babbar ofisan, lura da cutar shanyewar jiki, Rita Melifonwu, tace yawancin ma’aikatan lafiya na kasar nan na bukatar koyarwa akan kulawa da masu fama da shanyewar jiki. Ta kara da cewa yawancin su, hade da likitoci, basu da isashiyar kwarewa kan wannan.

Tace, “Muna bukatar sa hannun masanan lafiya na kowanne sashi don kulawa da shanyewar sashen jiki, kungiyar da zata hada da likitoci, malaman jiyya, masu bincike da sauransu. Rashin wannan shi yasa har yanzu mutane suke mutuwa a asibitai.”

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG