Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Bata Morar Zafin Rana Wajen Samun Makamashi


Tashar makamshi ta zafin rana dake ba wata karamar hukuma lantarki
Tashar makamshi ta zafin rana dake ba wata karamar hukuma lantarki

Jamhuriyar Nijar dai na daga cikin jerin kasashe bakwai na Afirka da masana suka bayyana a matasyin kasashen da suka fi samun karfi da hasken zana a duk fadin duniya musamman a yankunan Diffa da Agades

A yankunan Diffa da Agades tururin rana nada karfin gaske to sai dai kasar Nijar bata moran wannan abun da Allah ya bata wanda kuma arziki ne.

Kwararru sun ce yin anfani da karfi da hasken rana wurin samar ma kasar makamashi ita ce hanya mafi sauki da alfanu. Kasar zata samu wutar lantarki a saukake idan tayi anfani da zafi da hasken rana domin ta samu ta kawar da matsalar wutar lantarki da yanzu ta ke fama dashi.

Shugaban kungiyar kodaye mai fafutikar kare hakkin jama'a a fannin makamashi, Alhaji Mustapha Kadi Ummani, yace masu ilimi gaba daya na duniya sun amince da cewa idan kasar tana son ta rage zafin rana to sai an bar yin anfani da wutar lantarki ta inji. Zafin rana ba sayensa ake yi ba. Allah ne ya ba dashi. Yin anfani da wutar zafin rana tana kawo wa jiki lafiya da kasa baki daya saboda bata gurbata muhalli.

Shi ma Abdu Alhaji Idi wani mai bin digdigin alamuran yau da kullum ya danganta rashin samarda makamashi daga zafin rana da halayen shugabannin da suka shude ne. Yace sun fada tuntuni cewa yayin yin anfani da wutar injina ya wuce. Kamata ya yi a maida hankali wurin yin anfani da rana. Samun makamashi ta zafin rana ya zama rigar zamani, a saki a huta. Saboda haka wajibi ne su yi koyi da takwarorinsu na Morocco wadda ta yi anfani da zafin rana wajen samun makamashinta.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG