Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Jam'iyyar MNSD NASARA Ta Gana Da 'Yan Jarida


Shugaba Mahammadu Issufu na Nijar
Shugaba Mahammadu Issufu na Nijar

A karon farko tun bayan cika shekaru biyu da Shugaban Janhuriyar Nijar Mahammadu Issufu ya yi bisa gadon mulki, jam'iyyar adawa ta MNSD NASARA ta gana da 'yan jarida

Jam'iyyar adawa ta MNSD NASARA ta gana da 'yan jarida a karon farko tun bayan cika shekaru biyu da Shugaba Mahammadu Issufu ya yi bisa gadon mulki, inda ta yi zargin cewa Nijar ta gamu da matsaloli da kuma saba ma dokokin kasa saboda rashin iya mulkin Shugaba mai ci.

Kakakin jam'iyyar adawar ta MNSD NASARA Honorabul Tijjani Abdulkadiri ya ce a wannan karon ma ba za su shiga gwamnatin rikon kwarya ba ko da shugaban ya sake kiransu kamar yadda su ka ki a baya saboda har yanzu gwamnati ba ta iya shugabanci ba.

To amma da ya ke mayar da martani wani kusa a jam'iyyar PNDS TARAYYA mai mulki mai suna Alhaji Asumanou Mahammadu ya yi watsi da zargin na jam'iyyar ta adawa, ya ce an sami cigaba sosai musamman ma ta fuskar kare hakkin 'yan kasa da kuma tattalin arziki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG