Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Rikicin Jam'iyyar CDS Rahama Ya Kara Dagulewa


Mr.Morou Amadou, ministan shari'a na kasar Nijar
Mr.Morou Amadou, ministan shari'a na kasar Nijar

A Jamhuriyar Nijar ayayinda rikicin shugabancin jam’iyar CDS RAHAMA ke kara zurhi tsakanin bangarorin dake tafka mahawara a kotu daya bangaran jam’iyar ya tsayar ALHAJI ABDU LABOminista a fadar shugaba ISUHU MAHAMADU domin neman shugabancin kasa a zaben badi. Abinda masu rajin kare demokradiya ke dauka tamkar fatali ne da hukunce hukuncen kotu.

Cikin wani yanayi na kila wa kala ne bangaran na ABDU LABO ya soma wannan taron congres sanadiyar matakin haramcin da alkali ya dauka da farkobiyo bayan karar da tsohon shugaban kasa ALHAJI MAHAMAN USMAN ya shigar to amma daga bisani kotun daukaka kara ta bada iziningudanar da taron kamar yadda dan takarar da aka tsayardomin neman shuganbancin NijarministaABDU LABO ya bayyana.

Sai dai masu rajin kare demokradiya irin su ALHAJI SALISU AMADU na kungiyar Sauvons le Niger na ganin bangaran na LABO bai mutunta tsarin shara’a ba.

Minista ABDU LABO ya zauna gidan kasoa watannin baya saboda zarginsa da hannu a harakar sayan jarirai kafin daga bisani a bada bailinsa saboda haka na tambayeshi shin ba ya ganin wannan zai kawo cikas ga takararsa ?

Ya zuwa yanzu bangaran tsohon shugaban kasa Mahaman Usman bai ce komai ba akan wannan sabon mataki yayinda ABDU LABO da makardabansa suka fara kiraye kirayen a hada kai a fidda jam’iyyar CDS RAHAMA a zabubukan da za’a yi a shekara mai zuwa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG