Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Kafa Rundunar Zaratan Sojojin Da Zata Kakkabe 'Yan Ta'ada Daga Yankin Tillabery


Wasu dakarun Nijar
Wasu dakarun Nijar

'Yan ta'adda dake fitowa daga kasar Mali suna shiga kasar Nijar ta yankin Tillabery ta sa gwamnatin jamhuriyar Nijar kafa rundunar zaratan sojoji mai dakaru 245 da zata yaki tsageran a duk sadda suka shiga

Yin la'akari da yadda 'yan ta'adda suke son mayar da yankin Tillabery tamkar wani wurin da sukan iya su ci karensu ba babbaka ya sa hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijar sake jan damara domin yin gagarumar kakkabe ta hanyar yin amfani da wata sabuwar rundunar soji.

Sojojin su kimanin 245 zasu kasance dakarun Nijar zalla, ba zasu hada da sojojin wata kasa ba.Tuni ma suka fara sintiri a kowane sako na yankin Tillabery dake makwaftaka da kasar Mali.

Nasiru Sedu na kungiyar talakawa ya yaba da matakin. Yana mai cewa kwana kwanan nan kowa ya san irin harin da aka dinga kai masu a yankin.Yace matakan da da aka dauka sun nuna cewa dole ne sai an kara daukan wasu domin a shawo kan lamarin a samu a kare rayuka da lafiyar jama'a. Yace duk inda ta'adanci yayi kamari dole a tura sojoji su kula da wurin. Yace abu ne da 'yan kasa ya kamata su yaba dashi. Ya kira talakawa su taimaka wurin bada bayyanai domin taimakawa jami'an tsaro.

Wannan sabon shirin ya soma tasiri saboda an rufe kasuwanni da dama da aka ce 'yan ta'adan Mali na yin anfani dasu inda suke samun guzurin abubuwan da suke bukata. Haka kuma dubun masu hada baki da 'yan ta'adan ta cika bisa ga kayayyaki da dama da aka kama inji hukumomin Nijar.

Abdu Alhaji Idi mai nazari akan alamuran yau da kulllum na cewa da ma su ne 'yan Nijar yakamata su fidda kudi su kare kansu da kansu ba wasu ba daga waje.

Makon jiya ministan tsaron kasar Nijar Kalla Mukhtari ya ziyarci sansanin askarawan dake garin Tilua na yammacin Walam domin tabbatar da an zartas da duk matakan da gwamnati ta bukaci a dauka saboda a yi anfani da damar a karawa dakarun kwarin gwuiwa.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG