Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Lashi Takobin Daidaita Farashin Magunguna


Taron masu aikin kiwon lafiya da sayar da magunguna da gwamnatin kasar ta shirya
Taron masu aikin kiwon lafiya da sayar da magunguna da gwamnatin kasar ta shirya

A wani taron ma'aikatan kiwon lafiya da masu sayar da magunguna da gwamnatin jamhuriyar Nijar ta shirya ta zargi masu sayarda magunguna da kaucewa ka'idojin da aka basu kuma ta lashi takobi sai ta daidaita lamarin

Bayanai daga hukumomin kiwon lafiya na kasar Nijar sun yi nuni da cewa masu dakunan sayar da magunguna suna fatali da tsarin farashin sayar da kayansu a hukumance.

Ministan kiwon lafiya Dr. Iliyasu Idi Mainasara yace daga cikin masu zaman kansu shagon wata daya tak ke mutunta tsarin da gwamnati ta basu lamarin da yace gwamnati ba zata lamunta dashi ba.

Amma masu dakunan sayar da magunguna sun ce banbancin farashi tsakaninsu ba abun mamaki ba ne.

Hajiya Nana Aisha daya daga cikin masu dakunan sayarda magunguna tace farashi abu ne mai wuyar al'amari. Tace a wani shagon za'a tarar duk masu aiki a wurin kwararru ne. Wani kuma zai sa 'yan makaranta ne suna aikin ya biyasu kudi kalilan. Irin wannan ke kawo banbancin farashi.

A wani bangaren kuma masu sayen magani suna zargin ana yin sakaci tare da nuna rashin sanin aikin sosai. Wani Sule Maje ya bayyana irin abun da ya faru dashi sanadiyar sakaci da aka yi wurin da ya sayi magani.Yace ya tafi da takardar maganai da likita ya rubuta masa. Ya sayi maganin amma bayan kwana guda sai bakinsa ya soma bushewa. Sai da likita ya gaya mashi an yi kuskure a shagon da ya sayar masa da maganin. Yanzu maganar ta zama ta shari'a.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG