Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR : Ana Nazarin ba Mata Masu Juna Biyu Magani Kyauta


Matsalar ta mata masu ciki dai na matukar shafar jariransu.
Matsalar ta mata masu ciki dai na matukar shafar jariransu.

A jamhuriyar nijer jami’ai a ma’aikatar kididiga ta kasa da hadin guiwar takwarorinsu na kiwon lahiya sun fara nazarin wani rahoton bincike akan shirin bada magani kyauta ga mata masu juna biyu da yara kanana da zummar magance matsalolin dake kawo cikas ga tafiyar shirin wanda gwamnatin kasar ta kaddamar a shekarar 2006.

Sakamakon korafe korafen da jama’ar Nijar ke yi akan rashin cin moriyar shirin bada magani kyauta ga mata masu juna biyu da yara kanana ne ya sa gwamnatin kasar bada umurni gudanar da bincike don gano gaskiyar lamari.

Binciken wanda aka gudanar a jihohi 5 daga cikin 8 na kasar ya gano cewa gwamnati da jami’an kiwon lafiya kowa na da hannu wajen tauye tafiyar wannan shiri da ke da manufar tallafawa talakawa.

Malan Abubakar Maiyaki, jami’i a ma’aikatar kididigar jamhuriyar nijer ya yi karin bayani. Yace abinda suka binciko ya nuna cewa, jami’an dake aiki a cibiyoyin basu aiwatar da shirin bisa tsari. Banda haka kuma ana bukatar gwamnati ta rika biyan likitoci kudin da aka sayar da magani domin su samu su sake sayen wani magani da shi. Saboda haka yace akwai bukatar duba bangaren gwamnati da kuma likitoci domin kowanne yayi aikinshi yadda ya kamata.

Bisa ga bayanan malaman kiwon lafiya, rashin fahimtar tsarin tahiyar wannan shiri daga bangaren al’uma na daga cikin dalilan da suka haddasa cikas wa dorewarsa.

Bayanai na cewa bashin miliyan kusan dubu 20 ne asibitoci ke bin gwamnati a matsayin kudaden magungunan da aka baiwa talakawa kyauta a karkashin wannan shiri yayinda a daya gefe ake zargin wadansu asibitocin da laifin rubuta farashin da ya zarta na magungunan da suke bayerwa a zahiri lamarin da ake ganin shine masababin tsayarwa wannan shiri a galibin asibitoci mallakar gwamnati.

Ga rahoton da wakilin muryar amurka SULE MUMUNI BARMA ya aiko mana daga Yamai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG