Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Shawarci Gwamnatin Trump Kan Koriya Ta Arewa


Tsohon shugaban Amurka Barack Obama, ya shawarwaci magajinsa kafin ya sauka cewa ya nemi karin goyon bayan China, wajen shawo kan Koriya ta arewa game da shirin Nukiliyar kasar, kamar yadda wani tsohon jami'i a gwamnatin Obama- Jon Wolfsthal, wanda yake da masaniya game da batun ya fada.

Wolfsthal, yace a wata ganawa tsakanin tsohon shugaban na Amurka da Mr.Trump, ya gayawa masa cewa tilas sabon shugaban ya tunkari barazanar Nukiliya da makamai masu linzami daga Koriya ta Arewa.

Kamar yadda Mr. Wolfsthal yayi bayani, gwamnatin Obama ta gabatarwa Trump zabi biyu wajen tunkarar barazana daga koriya ta arewa, na daya ta wajen gudanar da shawarwari da kasar kai tsaye,ko kuma a kara matsin lamba kan koriya ta arewa ta matsawa uban dakinta China lamba.

Muriyar Amurka ta nemi majalisar tsaron kasa ta bata takaitaccen bayani kan manufofin sabuwar gwamnatin kan koriya ta arewa, amma har yanzu bata sami amsa ba.

Mr. Wolfsthal dai ya rike mukamin hadimi kuma babban darekta kan kayyade hayayyarfar makaman kare dangi a majalisar tsaron kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG