Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Da China Zasu Sanya Hanu Kan 'Yarjejeniyar Cinikayya Ta Dala Milyan Dubu Tara


Frimiyan China Wen Jia Boa yake duba faretin girmamawa da aka yi masa a Pakistan a fara rangadi a kasar jiya Jumma'a.
Frimiyan China Wen Jia Boa yake duba faretin girmamawa da aka yi masa a Pakistan a fara rangadi a kasar jiya Jumma'a.

Asabar din ake sa ran kasashen biyu zasu sanya hanu kan wan shiri,a ci gaba da rangadin da Frimiyan China Wen Jia Bao yake yi a Pakistan.

Asabar din ce ake sa ran Pakistan da China zasu rattaba hanu kan Karin wata yarjejejiniyar cinikayya ta dala milyan dubu 10, a ci gaba da rangadi da Frimiyan China Wen Jia Bao yake yi a Pakistan.

Jiya jumma’a ce China da Pakistan suka rattaba hanu kan yarjejeniyoyi daban daban har 13 gameda tattalin arziki. Ministan yada labarai na Pakistan Qamar Zaman Kaira,yace China ta amince ce zata tallafawa Pakistan da kudi dala milyan metan da 29 domin ta yi aikin sake farfado da sassan kasar da amabliyar ruwan ya yi wa barna,da kuma rancen dala milyan dari hudu.

Baki daya dai Kaira yace China zata samar da kudade domin ayyuka daban daban 36 da zasu ci kudi dala milyan dubu 14. Kodashike ziyarar Mr.Wen ya fi mai da hanakali kan cinikayya, ziyarar ta kara habaka dankon zumunc tsakanin kasashen biyu.

XS
SM
MD
LG