Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Zata kauracewa Taron Kasa Da Kasa Kan Afghanistan


Mutane Suke addu'o'i ga sojojin Pakistan Da harin NATO ya kashe.
Mutane Suke addu'o'i ga sojojin Pakistan Da harin NATO ya kashe.

Shugabar Jamus Angela Merkel ta bayyana fatar Pakistan zata sake shawara data yanke na kauracewa taron kasa da kasa da ake kudurin za a yi a Bonn kan makomar Afghanistan.

Shugabar Jamus Angela Merkel ta bayyana fatar Pakistan zata sake shawara data yanke na kauracewa taron kasa da kasa da ake kudurin za a yi a Bonn kan makomar Afghanistan.

Madam Merkel ta fada talatan nan cewa gwamnatinta zata yi bakin kokarin ta shawo kan jami’an Pakistan su sake wan nan shawara,wadda ta yanke sakamkon farmakin da dakarun kungiyar tsaro ta NATO suka kai wadda ya kashe sojojin Pakistan 24 a makon jiya a kan iyakar kasar da Afghanistan.

Yau talata Pakistan ta bada snarwar zata kauracewa taron. Jami’an Amurka da Afghanistan sun yi kira ga Pakistan ta halarci taron, wacce aka shirya da nufin daita daita al’amaru a kasar a dai dai lokacin da sojojin taron dangi suke shirin janyewa daga kasar cikin shekaru masu zuwa.

Shugaban rundunar mayakan Amurka ya fada jiya litinin cewa babu laifi idan Pakistan ta fusata kan farmaki da jiragen yaki kan wasu wuraren tsaro kan iyakarta da aka yi ya ranar Asabar. Sai dai bai nemi gafara kan wan nan lamari ba.

A hira da yayi da tashar talabijin ta Ingila ITV, babban hafsan hafsoshin Amurka Janar Martin Dempsey, yace akwai hujjar Islamabad ta fusata ganin makaman da suka kashe mayakan nata daga kawarta ce.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG