A wata hira da yayi da manema labarai jiya a birnin Moscow, shugaba Putin yace kasidun da aka baza a cikin makon jiya inda ake zargin Trump da wasu aiyukkan batsa a can Rasha,, duk wani bangare ne na kokarin da gwamnatin Amurka dake barin gado take yi na neman sa a rena kurar sabuwar gwamnatin ta Trump, a nuna kamar ba halatacciyar gwamnati bace.
Putin yace karya ce ake shatawa da rahottanin da ake yayatawa cewa wai Trump yazo Moscow a shekarar 2013, har yayi wata mu’amilar banza da karuwai a wata otel.
Putin yace masu baza irin wannan karyar sun ma fi karuwan rashin mutunci da rashin kima a idon kasashen duniya.