Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Fadakarwa Kan Illar Taba Sigari


Karan Taba Sigari
Karan Taba Sigari

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ware duk ranar 31 ga watan Mayu, domin fadakar da jama'a akan illar shan taba sigari a tsakanin al'umma.

A wani kiyasi da hukumar lafiya ta duniya ta fitar ya nuna cewar kimanin mutane Miliyan Shida ne ke mutuwa a duk shekara, a dalilin kamuwa da cututtuka dake da nasaba da shan taba sigari.

Taken bukin na bama dai shine hana yiwa kwalayen sigari kwalliya domin rage sha’awarsu, abinda hukumar lafiya ta duniya tace zai taimaka wajen rage shan taba sigari a duniya.

Shugabar hukumar lafiya ta duniya Margaret Chan, tace fatan hukumar shine ganin cewa gwamnatoci daban daban na kasashen duniya sun sa ido kan kamfanonin taba sigari don ganin sun rage irin adon da sukeyi kan kwalayen sigari, ta yadda hakan zai rage daukar hankalin jama’a musamman ma matasa wajen zukar tabar sigari.

Kawo yanzu dai binciken Likitoci ya nuna cewa tabar sigari na kunshe da akalla sinadarai kimanin 600 wanda kuma idan aka kona zasu fitar da wasu sinadarai kimanin 7000 masu cutarwa ga bil Adama, wanda kuma akasarinsu ke haifar da cutar daji wato Cancer a turance.

Sai dai masu iya magana na cewa idan kunne yaji to jiki ya tsira.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG