Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Inganta Harsunan Uwa a Duniya


UNESCO
UNESCO

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ware duk ranar 21 ga watan Fabarairu a matsayin ranar inganta harshen uwa a Duniya.

Hukumar bunkasa ilimi da Kimiyya da kuma Fasaha da al’adu ta MDD, UNESCO ta ware wannan rana ne domin ingatanta harshen uwa a Duniya. Take bukin na bana dai shine amfani da harshen uwa wajen koyarwa ta fannoni da yawa.

Mataimakin shugaban jami’ar ‘daukan darasi daga gida da ake kira National Open University of Nigeria, Farfesa Abdalla Uba Adamu, yace amfani da harshen uwa wajen koyawa yara karatu ya da amfani da kuma kalubale. Amfaninsa shine da’da inganta muhimmancin harshen uwa.

Gwamnatoci da hukumoni daban-daban a Najeriya da sauran kasashe ke bayyana muhimmancin amfani da harshen uwa wajen ‘daukar darasi da kuma amfani da harshen a harkokin yau da kullum.

Masana harsuna sun bayyana cewa yara ‘yan makaranta sunfi ‘daukar darasi a lokacin da ake koya musu da harshen uwa, wato harshen da suka tashi da shi a gidajensu.

Shugabar hukumar kula da al’adu da ilimi ta MDD ta UNESCO, malama Irina Bokova, tayi kira da hukumomi da gwamnatoci daban-daban da su tashi tsaye wajen ganin ana koyarwa da yara darusa cikin harsunan uwa, ta yadda zasu fahimci darussan cikin sauri.

Domin karin bayani ga rahotan Babangida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG