Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Iyaye Mata


Uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama a lokacin da ta kai ziyara a ranar bikin iyaye mata
Uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama a lokacin da ta kai ziyara a ranar bikin iyaye mata

A Amurka da wasu kasashen duniya, yau ce ranar da aka ware ta iyaye mata, domin a jinjina musu kan irin jan aikin da su ke yi.

Kamar yadda tarihi ya nuna, ranar ta zama hutu a Amurka ne, tun daga shekarar 1914 saboda irin jajircewan da wata mai suna Anne Jarvis ta yi wajen ganin an maida ranar a matsayin lokaci da za a jinjinawa irin sadaukarwar da mata iyaye ke yi saboda ‘ya’yansu.

Da farko dai ita Jarvis ta himmatu ne akan ranar ta zamo a matsayin wani lokaci mai muhimmanci tsakanin iyaye mata da iyalansu

Amma bayan da hukumomi suka tsaida ranar a matsayin ranar hutu, sai masu sayar da furanni da kamfanonin da ke buga katuna da sauran ‘yan kasuwa, suka himmatu wajen neman riba a lokacin bikin.

Hakan ya sa Jarvis ta nuna bacin ranta, ta kuma yi kira ga gwamnati da ta soke hutun wannan rana, kafin ta rasu a shekarar 1948

Sai dai ba a duk kasashen duniya ake bikin wannan rana ta iyaye mata a watan Mayu ba, a kasashe irinsu su Thailand sai a watan Agusta ake bikin, yayin da a Ethiopia ko kuma Habasha, ake bikin a lokacin hunturu domin karrama iyaye mata.

XS
SM
MD
LG