Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Na Kafa Sansanin Mayakan Yakin Sama a Syria


Shugaban Rasha Vladiir Putin
Shugaban Rasha Vladiir Putin

Ma’aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da rahoton da ya nuna cewa kasar Rasha na kafa sansanin yakin sama a Syria. Kamar yadda Kakakin cibiyar tsaro ta Pentagon Jeff Davis ya fadawa manema labarai a jiya Litinin.

Balaguron sojojin Rasha da na’urorinsu zuwa kusa da birnin Latakia da ke gabar teku ya nuna haramar Rasha a fili ta kafa sansanin sojin. Wani kamfanin dillancin labaran yammacin duniya ya rawaito wani jami’in Amurka na cewa,

Rasha ta aike da bindigogin yaki da kuma tankokin yaki samfurin T-90 guda 7 a sararin sojan saman Syria din dake Latakia. Pentagon tace, a makon da ya gabata ne Rasha ta yi jigilar kai sojojin ruwa guda 200.

Hade da gidajen da ake hadawa na tafi da gidanka da zasu iya daukar akalla mutane 1,500 din da za su je Syria. Sun hada har da bindigogi da na’urorin harba kananan rokoki masu linzami da kuma tankokin yaki.

Jakadan Syria a Rasha Riad Haddad wanda a da ya karyata wanzuwar sojojin Rasha a kasarsa, an ji kuma yana fada kuma kamfanin dillancin labaran Rasha ya rawaito kalamansa na cewa sun fi shekaru 40 suna hadakar makamai da rundunar sojin kasar Rasha.

An ji shima Ministan harkokin wajen Rasha Sergie Lavrov yana cewa sun yi jigilar makamai zuwa Damascus ta Syria sannan za su ci gaba da yin haka, don a cewarsa sun je koyar da yadda ake sarrafa makamansu ne.

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana damuwarsa game da hada-hadar sojojin Rasha a kasar Syria. Wanda yace hakan na iya dakatar da Amurka da kawayenta daga taimakon da suke na kawo daidaiton dimukuradiyya a Syria.

XS
SM
MD
LG