Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha ta fara janye dakarunta daga kasar Syria


Shugasban Rasha Vladimir Putin yayinda yake bada sanarwar janye dakarunsa daga kasar Syria
Shugasban Rasha Vladimir Putin yayinda yake bada sanarwar janye dakarunsa daga kasar Syria

A wata sanarwar bazata shugaban kasar Rasha yace ya yanke shawarar janye dakarun kasarsa nan take kuma tuni wasu mayakan saman kasar suka kama hanyarsu ta komawa gida bayan sun kwashe watanni shida suna kai hari kan 'yan tawaye.

A Rasha ma'aikatar tsaron kasar ta fada yau Talata cewa, tawagar farko ta jiragen yakin kasar sun bar Syria, bayan sanarwar d a shugaban kasar Vladimir Putin ya yayi na janye dakarunsa daga kasar bayan watanni biyar da rabi da suka yi a kasar Sham ko Syria.

Jirgin ya tashi daga sansanin mayakan sama dake lardin Latakia dake yammacin kasar kan hanyarsa zuwa Rasha.

Jiya Litinin shugaba Putin yace, "galibin" mayakan Rasha dake sham zasu bar kasar ganin yanzu an cimma burin abunda ya kai su.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya ko MDD na musamman kan rikicin na Syria Staffan de Mistura, yau Talata ya yabawa matakin da shugaba Putin ya dauka yana cewa "wannan muhimmin ci gaba ne," ya bayyana fatar hakan zai taimaka gaya wajen shawarwarin sulhu da yake shiga tsakani a Geneva.

Jakadan Angola a Majalisar Dinkin Duniya Ismael Gasper Martins,wanda shine yake rike da kujerar shugabancin kwamitin sulhu na karba karba, yace wannan mataki da Rasha ta dauka, da kuma komawa kan teburin shawarwari dangane da rikciin na Syria, ya nuna cewa "akwai canjin yanayi da kwamitin sulhu, na fatar ganin an sami "sakamako mai kayu."

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG