Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Republicans zasu cigaba da zaben fidda gwani gobe


'Yan Republican da suka fito neman tsyawa zabe, wasu sun dakatar da neman goyon baya saura uku.
'Yan Republican da suka fito neman tsyawa zabe, wasu sun dakatar da neman goyon baya saura uku.

Gobe ne 'yan takarar neman shugaban kasar Amurka a karkashin jam'iyyar Rebuplican zasu sake fafatawa inda bisa ga alamu Donald Trump ne zai sake yin nasara duk da kushewar da ake yi masa

Yan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam’iyyar Republican na kusantar zaben fidda gwanin da za a yi a jihohi guda biyu masu tsauri wajen zabar dan takara da za a yi a ranar Talata mai zuwa, inda Attajiri Donald Trump da abokin hamayyarsa da ke biye da shi Sanatan Texas Ted Cruz za su fafata.

Akwai yiwuwar raba wannan karawa ta fidda gwani a jihohin, a yayin da kuri’un jihar yammacin Amurka ta Arizona a baya zasu iya baiwa Mista Trump karin dama, tunda an buga takardun kada kuri’ar da suka fito da sunayen wadanda suka ce sun janye daga takarar ta Republican.

Ted Cruz dai ya nuna cewa shi kadai zai iya kada Trump, to amma akwai yiwuwar Donald ya lashe da samun gaba dayan wakilai 58 a gangamin na Republican, inda jam’iyyar zata zabi wanda zai mata takarar shekarar nan ta 2016. Kuri’un jin ra’ayi kuma sun nuna yiwuwar Ted zai iya cin zaben jihar Utah, wata jihar a yammacin Amurka.

Daga Trump har Cruz duk sun yiwa masu zabe alkawurran magance matsalar kwararar bakin haure zuwa cikin Amurka idan suka kai ga samun shugabancin kasar. Sai dai ba a zaton dan takarar da ke binsu a baya kuma gwamnan jihar Ohio John Kasich zai yi wani katabus a zabukan jihohin.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG