Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin PDP Sai Kara Ruruwa Yake Yi


Wasu shugabannin PDP
Wasu shugabannin PDP

Ambassador Kazauri mataimakin shugaban PDP na kasa ya ce da wuya a shawo kan rikicin PDP idan ba an koma kan bin tafarakin tsarin gudanar da jam'iyyar ba.

Ambassador Kazaure yayin da yake jawabi ya yi misali da Kano inda shugabancin jam'iyyar na kasa ya nuna halin mulkin kama karya da ko in kula.

Kamar yadda ya bayyana shugabannin jama'iyyar na Kano su suka rubutawa majalisar zartaswa ta kasa ta jam'iyyar cewa lokacinsu ya kare don haka a gaya masu ranar da za'a yi sabon zabe da yadda za'a yi zaben. Sun rubuta wasikar ne tun kafin rigimar jam'iyyar ta barke. Amma ba'a yi komi ba sai bayan da rigima ta kunno kai shugabannin jam'iyyar na kasa suka kafa kantoma abun da babu shi a kundun tsarin gudanar da jam'iyyar.

Ambassador Kazaure ya ce idan Bamanga Tukur na son ya rika nada abokanansa kan mukami jam'iyyar PDP yanzu tafi karfin haka.Lokacin nada abokai ya wuce. Dole a bi tsari, a yi zabe kafin kowa ya dare kan kowane mukami. Yanzu maganar ta rincabe a Kano domin an kai shi Ambassador Kazaure kotu da kantoman da Bamanga ya nada da sakataren kantoman da shi Bamanga Tukur. Irin wannan dagulewar ba zata haifar da da mai ido ba.

A halin yanzu babu batun sasantawa sai an yi gaskiya an bi abun da kudun tsarin mulkin jam'iyyar ya ce a yi. Ya ce ana shirin sasantawa amma wadanda basa son jam'iyyar ta gyaru suna dada kawo baraka domin sun san yin sulhu zai kawo masu asara.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG