Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Ta Ce Ta Kashe 'Yan Boko Haram Da Dama A Wani Hari Ta Sama


Kakakin rundunar sojojin, Kanar Mohammed Dole, yace jiragen saman yaki sun yi luguden wuta kan 'yan Boko Haram a lokacin da suke kokarin jana'izar 'ayn'uwansu da aka kashe

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne a wani farmakin da aka kai ta sama a kan masu kokarin yin jana'iza a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kakakin runduna ta 7 ta sojojin Najeriya mai hedkwata a Maiduguri, Kanar Mohammed Dole, ya fada asabar din nan cewa 'yan kungiyar Boko Haram su na tilastawa matasa shiga cikin kungiyar da karfi, sannan su na sace mata, amma dakarun tsaro su na bin sawunsu.

Kanar Dole yayi ikirarin cewa wani farmakin da sojoji suka kai cikin 'yan kwanakin nan ya yi barna mai yawan gaske ma mayakan Boko Haram.

Farmaki ta sama da aka kai ranar jumma'a, shi ne harin jiragen sama na farko da aka bayar da rahoton kaiwa tun makon jiya, a lokacin da mayakan Boko Haram suka kai wani farmaki, suka cinna wuta a wasu sansanonin soja guda biyu dake Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, inda suka lalata wasu jiragen kai farmaki uku da helkwafta guda biyu.

'Yan jarida sun ga wani jirgin saman yaki yana tashi daga Maiduguri a jiya jumma'a, a lokacin da Kanar Dole yace barin wutar da jirgin yayi ya kashe mayakan Boko Haram da dama wadanda suka je suke kokarin binne 'yan'uwansu da aka kashe.

Dubban mutane sun rasa rayukansu a wannan yamutsi na Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
XS
SM
MD
LG