Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Ta Sayo Sabbin Makamai


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Babban hafsan sojojin mayakan kasa na Najeriya Lt Janal Tukur Yusuf Buratai, yace nan bada jimawa ba zasu kawo karshen ‘yan Boko Haram, da yanzu haka yace sun riga sunci karfin su.

Janal Burutai yace ko a yanzu haka rundunar sojan ta samu kwato wasu Kauyuka da dama da kubuto da wasu mutanen da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su, musammam ma a garin Kumshe dake karamar hukumar Bama. Burutai dai ya nunawa yan Jarida wasu jiragen sama dake shawagi ba tare da matuka ba wanda ake kira Drones a turance, da rundunar sojan ta sayo, kuma zata yi aiki dasu wajen gano mahara da kawo karshen su ba tare da bata lokaci ba.

Haka kuma an nuna wasu manya manyan bindigogi ga ‘yan Jaridun, wanda suma aka ce za a yi amfani da su wajen kawo karshen yan ta’addan.

Rundunar dai ta gana da kungiyar dattawan jihar Borno cikin sirri, hakan ne yasa wakilin Muryar Amurka neman jin abinda aka tattauna akai amma shugaban kungiyar Ambasado Gaji Galtimare yace batu ne na sirri da bai kamata fadawa manema labarai ba.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG