Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Zata Sako Fursunonin Boko Haram 167


Sojoji da 'yansanda sun shiga sintiri bayan harin da ake zato 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kusa da sansanin mayakan sama a Maiduguri ranar 2 ga watan Disamba shekarar 2013.
Sojoji da 'yansanda sun shiga sintiri bayan harin da ake zato 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kusa da sansanin mayakan sama a Maiduguri ranar 2 ga watan Disamba shekarar 2013.

Wadannan fursunoni sun a daga cikin mutanen da sojoji suka kama suka tsare a ci gaba da yakin da suke yi da Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya

Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar jumma’a cewa zata sako mutane 167 wadanda aka tsare a wani bangare na yaki da kungiyar Boko Haram a wasu jihohi uku na yankin arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya, Birgediya-Janar Chris Olukolade, yace fadar shugaban Najeriya ce ta bayar da umurnin sakin mutanen, a bayan shawarar da wata hukuma ta bayar a watan Disambar da ya shige.

Za a sako mutane 157 daga sansanonin soja a Jihar Borno, 9 daga jihar Yobe da kuma guda 1 daga Jihar Adamawa. Dukkan jihohin guda uku sun kasance karkashin dokar-ta-baci tun watan Mayun shekarar da ta shige.

Kakakin ya fada cikin wani sakon da ya tura ta Imel cewa, “za a mika mutanen ga gwmnatocin jihohinsu.”

A ranar 4 ga watan Disamba, Najeriya ta bayyana cewa zata gabatar da mutane 500 daga cikin mutane kusan dubu daya da dari hudu da aka kama daga Yuli zuwa Satumbar bara a gaban shari’a, bisa tuhumar aikata laifuffukan ta’addanci.

Amma kuma ta ce za a saki 167 daga cikin wadanda aka kama, yayin da za a sake nazarin batun sauran mutanen su 614, a bayan da wata hukumar da gwamnati ta kafa domin nazarin matsayin dukkan mutanen da aka kama ta bayar da shawarar yin hakan.

Gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta bayyana a watan Mayun bara cewa za a saki mutanen da aka kama a sanadin matakan soja da ake dauka, amma za a sako su din ne daki-daki, inda za a fara da mata da yara.

Dubban mutane sun rasa rayukansu a tashin hankali mai nasaba da kungiyar Boko Haram a arewacin Najeriya, wasu a hare-haren mayakan kungiyar, wasu kuma a matakan martanin da sojoji ke dauka.

Sai dai kuma kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun jaddada batun yadda ake tilasta bacewar mutane tare da tsare mutane ba tare da tuhumarsu da aikata wani laifi ba, duk a bangaren matakan sojan da ake kara dauka a kan Boko Haram.

A watan Oktoba a bara, kungiyar Amnesty International ta ce mutane fiye da 950 sun mutu a hannun sojoji a watanni shida na farkon shekarar 2013, akasarinsu a cikin barikokin soja dake Maiduguri da Damaturu.
XS
SM
MD
LG