Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Sassauta Dokar Ta Baci A Jihar Adamawa


Komandar rundunar Sojojin da aka tura yola domim dokar tabaci, Birgediya General Fatai Oladipo Alli kuma brigade komanda na tankokin yaki yayiwa Sojojin jawabi kafin turasu bakin aikinsu. Hoto Ibrahim Abdul'Aziz
Komandar rundunar Sojojin da aka tura yola domim dokar tabaci, Birgediya General Fatai Oladipo Alli kuma brigade komanda na tankokin yaki yayiwa Sojojin jawabi kafin turasu bakin aikinsu. Hoto Ibrahim Abdul'Aziz

Rundunar Sojin Najeriya Ta Sassauta Dokar Ta Baci A Jihar Adamawa, daya daga cikin jihohi uku a arewa maso gabashin Najeriya da aka kakabawa dokar ta baci.

Rundunar Soji a Adamawa ta sassauta dokar ta baci a jihar Adamawa daya daga cikin jihohi uku da aka kakabawa dokar ta baci a arewa maso gabashin Najeriya, jihohin da suka hada da Adamawa, Borno da Yobe.

A wata sanarwa da rundunar ta ashirin da uku dake Yola babban birnin jihar ta ce dokar zata fara aiki ne yanzu daga karfe goma sha daya na dare zuwa karfe biyar na asubahi domin ba Musulman jihar damar yin azumi cikin walwala. Yayin da yake karin haske kakakin rundunar Kanal Ja'afaru Mohammed Nuhu ya ce al'umma su kiyaye doka domin zasu shiga wando kafa daya da duk wanda ya karya doka. Ya ce su zauna inda aka ce su zauna. Kada kuma su fita lokacin da bai dace ba.

Sassautawar ta zo daidai da lokacin da kwamitin dake neman sulhu da kungiyar Boko Haram wanda ke karkashin jagorancin ministan ayyuka na musamman Alhaji Tanimu Turaki ke kammala ziyarar da ya kai jihar ta Adamawa.Yayin ziyarar kwamitin ya gana da sarakuna da shugabannin addini a jihar inda shugaban kwamitin yake yabawa sarakuna bisa ga matakan da suke dauka na kirkiro sarakunan matasa lamarin dake taimakawa wajan kawo zaman lafiya.

A wani lamarin kuma wasu kananan hukumomi sun soma taimakawa al'umma da dokar ta baci tafi shafa musamman masu karamin karfi yayin da suke kokarin kama azumi. Shugaban karamar hukumar Jada cewa ya yi idan ba'a taimaka ma irin wadannan mutanen ba suna iya zama sanadiyar kara tabarbarewar tsaro.

Daga karshe gwamnan jihar Murtala Nyako ya yaba da addu'o'i da ake yi ya kuma ce a cigaba da yin addu'a musamman cikin watan azumi.

Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG